Mai martaba Sarkin Zazzau a Jihar Kaduna Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya bukaci iyaye da masu kula da su da su tabbatar ‘ya’yansu sun samu ilimin boko da na addinin Musulunci.
Ya ce tarbiyyar yara ita ce mafi kyawun gadon iyaye da za su bar wa ‘ya’yansu domin su zama ‘yan kasa nagari.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Bukaci Daliban Jihar Ogun Su Fara Amfani Da Hijabi A Makarantun Jihar
Sarkin ya yi jawabi ne a wajen bikin cika shekaru dari na makarantar firamare ta LEA da ke Makarfi ta tsakiya da aka kafa a shekarar 1922 tare da dalibai 14.
Kungiyar Tsofaffin dalibai Maza na makarantar ne ta shirya taron a garin Makarfi.
A cewarsa, ya kamata a inganta makarantun gwamnati domin a nan ne akasarin al’ummar karkara ke sanya ‘ya’yansu don yin karatu.
“Dole ne mu tabbatar da cewa ‘ya’yanmu sun samu ilimin zamani da na addinin Musulunci domin su zama shugabanni nagari a nan gaba.”
“Idan ba ilimi ko na boko da na addinin Musulunci, rayuwa za ta yi wahala, don haka dole ne mu wayar da kan jama’armu don ganin sun samar da damammaki na ilimin ‘ya’yansu,” inji shi.
Sarkin ya ce bai taba zuwa makaranta mai zaman kanta ba, ya kara da cewa mafi yawan masu fada aji a yau suna zuwa makarantun gwamnati, don haka ya kamata a taimaka a gyara irin wadannan makarantu domin yaran masu karamin karfi su samu ilimi.
Sarkin Bamalli ya kuma yabawa tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmed Makarfi, wanda kuma tsohon dalibin makarantar LEA Makarfi ta tsakiya ne, bisa aiwatar da ayyuka da suka yaba a fadin jihar a lokacin da yake mulki.
Shugaban kwamitin shirya taron, Alhaji Suleiman Abdulkadir Garkuwan Zazzau, ya ce makarantar ta samar da mutane da dama wadanda suka rike mukamai a jiha da kasa tun bayan kafuwarta.
A wani labarin kuma, 2023: Atiku Ne Zai Lashe Zabe Tun A Zagayen Farko – PCC
Kungiyar yakin neman zaben Atiku/Okowa ta ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, zai lashe zaben shugaban kasa na 2023 tun a zagayen farko.
Kakakin kwamitin yakin neman zaben sa, Mista Kola Ologbondiyan, ya bayyana kwarin gwiwa a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata.