Satar Ɗanyen Mai: Dakarun Sojin sama sun lalata Haramtattun matatun mai guda 7 a Rivers
Rundunar Air Component Operation Delta Safe ta kai farmakin sama domin hana barayin man fetur da masu gudanar da ayyukan tace man ta haramtattar hanya, inda suka lalata Haramtattun wuraren guda 7 a Jihar Ribas a ƙarshen makon nan.
Daraktan hulda da jama’a da yaɗa labarai na NAF Air Commodore Edward Gabkwet ya ce an gudanar da kai farmakin ne a tashar Cawthorne da Bille duk da ke ƙaramar Hukumar Degema ta Jihar Ribas inda ya kara da cewa “An samu nasarar gano wuraren tace haramtattun wurare 7 tare da lalata su.
Har ila yau, Rundunar ta hana barayin mai damar fasa bututun mai tare da gudanar da ayyukansu na matatun man da suke yi ba bisa ka’ida ba tare da lalata dukkanin wuraren.
Air Commodore Gabkwet ya ce A cikin tashar Cawthorne Channel, an ga wuraren 4 da ke aiki ba bisa ka’ida ba, wanda ya haɗa da ramukan Mai, da tankunan ajiya da ake zargin suna ɗauke da Ɗanyen man da ba a ranar 15 ga watan Satumban shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN:Rashin tsaro: Kada ku bar duk wani Ɗan Ta’adda ya tsira a yankunan ku – CDS ya Umarci kwamandojin tsaro
Daga baya an lalata wuraren. Sannan kuma dakarun sun kai irin wannan harin ta sama a Bille a ranar 16 ga Satumba 2023 da kuma farkon 17 ga Satumban shekarar 2023.
A can ne aka lalata wuraren tace man da ba bisa ka’ida ba 3 da tankunan ajiya da kuma rami.
A ɗaya daga cikin wuraren, akwai wani jirgin ruwa na Cotono da ake zargin yana diban Ɗanyen mai daga tashar ruwa ya bi ta hanyoyi da dama wanda shima an lalata shi.
A cikin watanni 2 da suka gabata Kamfanin Cawthorne da Bille ne ke da alhakin mafi yawan satar mai da ayyukan tace mai da aka gudanar a Jihar Ribas.
A cikin wannan lokacin, sama da wuraren tace man fetur 30 a waɗannan wurare 2 ba bisa ka’ida ba ne Dakarun Sojin Ƙasa da na Ruwa da na sama suka lalata.
“Za a ci gaba da gudanar da wannan ƙoƙarin a waɗannan wurare da sauran su har sai barayin mai da ‘yan ta’addan su daina ayyukansu na haram”, inji shi.