Kasar Saudiya ta bude kan iyakokinta na sama, da ruwa da kuma na kan tudu tsakaninta da kasar Qatar tun daga ranar Litinin a wani matakin maido da dangantaka tsakaninsu dake kawo karshen zaman doya da manja na tsawon shekaru uku.
A ranar Talatar nan ne aka cimma yarjejeniyar maido da dasawar a taron shekara-shekara na kungiyar kasashen larabawa da suke yi a garin Al’Ula na kasar Saudiya, wanda Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani ya halarta.
Tun a shekarar 2017 kasashen Saudiya da Hadeddiyar Daular Larabawa da Masar da Bahrain suka kirbawa Qatar takunkumin hana cinikayya da kuma zuwa kasar, saboda zargin ta da marawa ta’addanci baya.
A baya-bayan nan Kasar Kuwait ta sanar da cewar kasashen dake yankin tekun Fasha za su gudanar da wani taro ranar 5 ga watan Janairu a Saudiyan wanda ake sa ran zai sasanta rikicin dake tsakanin Qatar da Saudiya.