Ministan wutar lantarki inijiniya Abubakar D. Aliyu, ya ce yanzu haka an kammala aikin samar da wutar lantarki na Zungeru kashi 96%.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki wajen aiki samar da wutar lantarki na Zungeru a jihar Neja.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Injiiniya Abubakar D. Aliyu ya kuma ce wutar lantarki ta Zungeru na daya daga cikin ayyukan da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta sa gaba. An saita aikin don ƙara megawatts 700 (zero carbon) a cikin layin grid na ƙasa.
KU KARANTA KUMA: An Inganta Wutar Lantarki A Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari
“An shirya kaddamar da aikin nan ba da dadewa ba, a wani bangare na kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na inganta wutar lantarki a fadin Najeriya da kuma cika alkawarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na samar da hangen nesa 30:30:30 da kuma cimma nasarar samar da wutar lantarki nan da shekarar 2060, kamar yadda ya yi alkawari a COP 26. ” Ministan ya kara da cewa.
Ya kuma kara da cewa gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa an samar da dukkan bukatun ‘yan kwangila domin ganin an kammala shi a kan lokaci.
Baya ga samar da karin wutar lantarki ga ‘yan Najeriya, Ministan ya ce a halin yanzu aikin yana samar wa ‘yan Najeriya aikin yi kuma za a rika daukar wasu ayyuka yayin da aikin ke tafiya.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Ministan ya samu rakiyar jami’an ma’aikatar wutar lantarki ta tarayya, ‘yan kwangilar da masu ba da shawara kan aikin. Ana shirin kaddamar da aikin nan ba da jimawa ba, kamar yadda ya bayyana.
Wutar Lantarki ta Zungeru wani shiri ne na ma’aikatar wutar lantarki ta Kasa.
A Wani labarin Kuma: Shawarwarin Amurka Da Burtaniya Bai Kamata Su Haifar Da Firgici Ba
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce sauye-sauyen da aka samu na shawarwarin tafiye-tafiye daga gwamnatocin Amurka da Birtaniya bai kamata su zama abin tsoro ba.
Shugaban kasar, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’ar nan ta hannun mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya shawarci jami’an tsaron kasar da daukacin al’ummar kasar da su ci gaba da yin taka-tsantsan da kuma kula da lamarin tsaro.