Sauya Matsugunin CBN da FAAN, Sanatocin Arewa sun buƙaci zama da Tinubu
Biyo bayan tofa albarkacin baki da al’umma ke yi akan shirin Gwamnati na mayar da wasu Manyan sassan Babban bankin Najeriya zuwa Legas da kuma hukumar kula da filayen jiragen sama ta Tarayya, kungiyar Sanatocin Arewa ta yi kira ga al’umma da a kwantar da hankula.
Kungiyar Sanatocin ta ce za a samu damar tattaunawa kan batun da ke cike da rudani tare da Shugaba Bola Tinubu inda suka bayyana shirinsu na tattaunawa da Shugaban ƙasar.
A wata sanarwa a ranar Litinin da ta gabata ta bakin Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu a madadin Kungiyar ta ce za a nemi mafita kan lamarin ta hanyar da ta dace idan aka kasa cimma matsaya.
Ya kuma tabbatar da cewa Kungiyar za ta ɗauki mataki daidai da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki na 1999 da aka yi wa kwaskwarima inda ya jaddada cewa babu wanda ya isa ya ji tsoro game da sauya ma’aikatun Gwamnati masu muhimmanci.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ɗaliban Wata Jami’a sun tare Makarantar, ba shiga ba fita saboda ƙarancin Wutar lantarki a Jami’ar
Sanata Kawu Sumaila wanda shi ne Kakakin kungiyar ya ce “Za mu haɗa hannu da ɓangaren zartarwa na Gwamnati da kuma Shugabannin Majalisar dattawa da masu ruwa da tsaki domin sauraren matsalolin ‘yan Najeriya da kuma samar da bayanai kan ci gaban da muka samu.
A matsayinmu na wakilan jama’a a matakin kasa (Majalisar Dattawa) mun himmatu wajen ganin an magance tabarbarewar rabe-raben kai, da rabon arzikin kasa a kasafin kudin 2024 da kuma mayar da wasu hukumomin tarayya daga Abuja zuwa Legas”.
A cewarsa an samu wasu kura-kurai a cikin manufofin Gwamnati wanda kungiyar ba za ta yi watsi da su ba amma za ta magance su ta hanyar kasafin kudi.
A wani labarin kuma:FCT: Wike ba ya amsa wasikun sakonnin da nake Tura masa” – Sanata Kingibe
FCT: Wike ba ya amsa wasikun sakonnin da nake Tura masa” – Sanata Kingibe
Sanata mai wakiltar Babban Birnin Tarayya Abuja, Ireti Kingibe, ta ce akwai rashin jituwa sosai tsakaninta da Ministan babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike da Shuwagabannin Siyasa waɗanda aka zaba a yankin.
Da take magana a gidan Talabijin na Channels a ranar Lahadi, Ƴar Majalisar da aka zaɓa a ƙarƙashin Jam’iyyar Labour Party (LP) ta ce “Ina da sakonnin WhatsApp ɗumbi da na rubuta masa, wasiku daya ko biyu amma sam ban samu amsa ba.”