Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya bayyana cewa sauya sheka da wasu gwamnonin jiha suka yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki ba barazana ce ga burinsa na siyasa ba, amma ya fi jin dadin samun su a jam’iyyar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, ta cikin wani shiri mai suna Sunrise Daily.
“Ina jin farin ciki maimakon a yi mini barazana. Burina yana hannun Allah, iko da buwaya na Allah ne.
“Yayin da muke da gwamnoni a jam’iyyar APC, za mu samu damar cin zabe. Da yawan damar da za mu samu na cigaba da ayyukan Najeriya daga inda Shugaban kasa zai tsaya nan da 2023,” Umahi ya mayar da martani lokacin da aka tambaye shi ko masu sauya sheka na yi masa barazana.
Umahi, wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar gwamnonin Kudu-maso-Gabas, shi ma ya yi magana a kan ziyarar da ya kai a fadar gwamnati da ke Abuja.
Ya bayyana cewa makasudin ziyarar ba wai kawai burinsa na zama shugaban kasa ba ne, har ma da batun tsaro da tattalin arzikin yankin kudu maso gabas.
“Batun ba wai kawai na je wurin Shugaban kasa ne na tambaye shi cewa ina son tsayawa takara ba. Akwai wasu batutuwa da yawa da na je don tattaunawa da Mista Shugaban kasa.
“Na je can ne domin tattaunawa kan yadda za a magance matsalar rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas, da kuma kan aikin filin jirginmu. Na je can ne don in sanar da shi cewa aikin filin jirginmu zai kasance a shirye a watan Mayu 2022 amma muna buƙatar taimakon kuɗi don siyan kayan aiki.
“Wannan shi ne abu na karshe da na ambata masa.
“Batun tsayawa takara a gefe ne, kuma na ambace shi a matsayin uban kasa kuma uban jam’iyyarmu ta siyasa.”
Umahi, a makon da ya gabata, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023 a fadar gwamnati da ke Abuja.
Sanarwar tasa ta zo ne kimanin sa’o’i 24 bayan tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, ya nuna sha’awarsa a takarar. Dukkan mutanen biyu ‘yan jam’iyyar (APC) ne mai mulki.