Jam’iyyar SDP a jihar Oyo ta dakatar da dan takararta na gwamna a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, Michael Lana, da sakataren jam’iyyar Idowu Owokoya, bisa zarge-zargen cin amanar jam’iyyar.
Dakatarwar tasu ta na kushe ne ta cikin wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar SDP na jihar Oyo, Michael Okunlade, kuma aka aika zuwa hedikwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Karya Ne Ortom Bai Bayar da Kwangilar Gina Filin Jirgin Sama Ba, PDP Ta Fadawa APC
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa an samu rashin jituwa tsakanin bangaren zartarwa na jam’iyyar da dan takararta na gwamna kwanaki kadan kafin zaben kan wanda zai ruguza tsarin jam’iyyar SDP wajen narkewa a tsakanin Seyi Makinde na jam’iyyar PDP da Teslim Folarin na jam’iyyar APC.
“Bayan nazartar ayyukan Lana, dan takarar gwamna a babban zaben da aka kammala, da sakataren jam’iyyar a lokacin zabe da kuma bayan zaben, majalisar ta yanke hukunci kamar haka:
“Cewa an dakatar da Lana daga jam’iyyar saboda ayyukan da ya yi na adawa da jam’iyyar. (Ba shi da) wani gagarumin gudumawa ga jam’iyyar. A dakatar da sakataren jam’iyyar na jihar Owokoya ne saboda rashin da’a, rashin biyayya, da kuma soke sunan sakatariyar jam’iyyar na kasa domin tada zaune tsaye.
“A bisa tsarin mulkin jam’iyyar, saboda haka, muna fatan mika kudurin jam’iyyar domin amincewar ofishin ku na dakatar da Lana da Owokoya. Jam’iyyar ta kuma yanke shawarar cewa Ajibola Adeniyi na karamar hukumar Lagelu a karkashin gundumar Oyo ta tsakiya zai maye gurbin Owokoya a matsayin mukaddashi.
“An gudanar da taron ne a ranar 31 ga watan Maris, 2023, a ofishinmu na jiha. Ya kunshi mambobin shugabannin zartarwa na jihohi da shugabannin kananan hukumomi,” kwafin wasikar ya karanta.
A wani labarin kuma, Kaduna: Takardar Shaidar Lashe Zaben Uba Sani Ta Wucin Gadi Ce – Shugaban PDP
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna, Mista Felix Hassan Hyet, a ranar Lahadi, ya ce takardar shaidar cin zabe da aka baiwa zababben dan takarar gwamna, Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC, na wucin gadi ne kawai, a matsayin wanda ya cancanta wanda ya lashe zaben, Isah Ashiru ne zai dawo da aikinsa ta hanyar kotun da ta dace.
DAILY POST ta tuna cewa dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Kaduna, Sani an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.