SHARI’AR KANO: “Kun san kun faɗi, Amma Ku kayi Yunƙurin ƙwatar Mulki da tsiya” – Lamiɗo
Tsohon Sarkin Kano Muhammad Sanusi II ya ce lokaci ya kure da dan Takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a zaɓen da ya gabata na Jihar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da sauran jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar su amince cewa shan kaye.
Sanusi ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ya yi magana kan karɓar ƙaddara a lokacin da yake gabatar da wani darasi.
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Dr. Abdullahi Ganduje na daga cikin jiga-jigan Jam’iyyar APC da ke neman Gawuna ya karɓi ragamar mulki a Jihar bayan da kotun Tirabunal da ta ɗaukaka ƙara ta kori Gwamna Kabiru Abba Yusuf na jam’iyyar NNPP.
Sai dai a ranar Juma’ar da ta gabata ne kotun kolin ta yi watsi da hukunce-hukuncen kananan kotunan.
KARANTA WANNAN:INEC ta fara tantance matsayin jam’iyyun siyasa
A wata hira da BBC Hausa, Gawuna ya ce ya amince da hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben Gwamna a Jihar a matsayin hukuncin da Allah ya zartas.
Amma da yake mayar da martani ga furucin Gawuna, tsohon Gwamnan Babban bankin ya ce APC ta yi yunkurin ƙwace Mulkin ne ta hanyar kotu ba tare da sanin Allah yana ji kuma yana gani ba.
Sanusi ya ce “Muna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki tare da taya al’ummar Jihar Kano murna a zaman da muka yi na ƙarshe, mun yi addu’a tare da gargadin alkalai da su yi abin da ya dace, daga ƙarshe Allah ya baiwa al’ummar Jihar Kano abin da suka zaɓa.
Lokacin da mutane suka kaɗa kuri’a duk wani yunƙuri na tauye zaɓin nasu zalunci ne aka so shirya wa daga sama.
“Sun shiga zaɓe, kuma sun sha kaye, amma sai suka yi kokarin bi ta hanyar gurbatattun alkalai, Wannan littafi da muke karantawa yana magana ne game da karɓar ƙaddara mai kyau ko mara kyau don yarda da hukuncin Allah” inji shi.
Wani abin dariya shi ne, bayan da wasu suka sha kaye a zabe sun garzaya kotu domin ƙwace mulki daga karshe dai a kotu sun gamu da Allah a jira bayan ya hana su samun mulki da ƙarfin tsiya, a yanzu sun ce sun amince da hukuncin da ya yanke.
Mafi kyawun lokacin da za a yarda da kaddara shine bayan zaɓen, Kun san mutane ba su zabe ku ba, Kun san kun yi rashin nasara amma kuka yi yunkurin kwace mulki, amma ku sani kun makara.
“Allah yana kan gaskiya a koda yaushe yana iya baiwa azzalumi dama, amma tabbas hakan ba zai ɗore ba.”
Sai dai Sanusi ya yi addu’ar samun nasara ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a cikin Mulkin shi, inda ya buƙaci Gwamnan da ya cika alkawuran da ya ɗauka a yayin yaƙin neman zaɓe.