Shugaban Kungiyar Yan shi’a ta IMN na Nigeria Sheikh Ibrahim El-zakzaky, yayi taro da wasu daga cikin wadanda suka tsira a lokacin da Yan shi’a suka yi arangama da Sojoji a watan Disamba na Shekarar 2015.
Zakzaky ya kuma gana da iyalan wadanda aka kashe a lokacin arangamar, kamar yadda majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaita.
Idan dai ba’a manta ba, Babbar Kotun Jahar Kaduna a ranar 28 ga watan juli na Shekarar 2021, ta sake shi tare da wanke shi da matar shi Zeenat, bayan gudanar da shari’a akan laifuka 8 da aka zargin shi da aikatawa, ciki harda ta’addanci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Filato: Dalibai Bakwai Sun Jikkata Yayin Zanga Zangar Dage Jarrabawa
Amma a lokacin da yake jawabi a Abuja, a cewar wata sanarwa daya baiwa majiyar Jaridar Dimokuradiyya, Sheikh ya yi amfani da wannan damar, wajen jajantawa wadanda suka rasa masoyan su a lokacin wannan arangamar data faru.
Ya bukace su da akoda yaushe su rika tunawa da wahalhalu da Imam Hussein(AS) ya fuskanta a hannun Sojojin Yazid wanda suka musguna masu tare da kashe shu.
Ya tunatar da wadanda suka ziyarce shi cewa, babu wata sadaukarwa da baza’ayi ba, idan ya kasance a tafarkin Allah akayi ta.
Sheikh Zakzaky ya kuma basu hakuri na gayyatar da yayi masu, maimakon zuwa gidajen su, tare da jajanta masu.
” A dalilin wasu raunuka da muka ji a lokacin farmakin sojoji akan mu, har yanzu muna dauke da harsashi a cikin jikinmu, to babu wata hanya da zamu iya zuwa ga kowane wanda lamarin ya shafa, da wanda suka tsira a kisan kiyashi na sojoji a watan Disamba na Shekarar 2015,” inji shi.
Zakzaky ya kuma yi addu’a ga Allah daya baiwa iyalansu juriyar rashin da suka yi, tare da yin addu’a ga Allah daya amshi shahadar wasu da suka mutu.
Dayake maida martani, Dr. Isa Waziri Gwantu, wanda yace ya rasa ‘ya’ya 4 a lokacin faruwar lamarin a Zaria, ya bayyana godiyar sa ga Shehin Malamin daya gayyace su.