- Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari mai barin gado ya bar Abuja zuwa jihar Katsina.
- Buhari ya hau jirgin rundunar sojojin saman Najeriya mai lamba 5N-FGW tare da matarsa da dansa da wasu mataimaka da misalin karfe 11:57 na safe.
- Tsohon Shugaban kasar ya samu rakiyar wasu daga cikin hadimansa.
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja zuwa jihar Katsina,The Nation ta rawaito.
Ya hau jirgin rundunar sojojin saman Najeriya mai lamba 5N-FGW tare da matarsa da dansa da wasu mataimaka da misalin karfe 11:57 na safe kuma jirgin ya tashi da misalin karfe 12:01 na rana.
KARANTA WANNAN: Yana Sauka Daga Mulki: Kamfanin Twitter Ya Cire Alamar Tantancewa A Shafin Osibanjo
Wani jirgin NAF mai lamba 5N-FGZ dauke da ‘yan uwa da sauran mataimaka shi ma ya tashi nan da nan bayan na farko.
Ya samu rakiyar tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da uwargidansa da kuma shugaban ma’aikatan fadar sa, Farfesa. Ibrahim Gambari, tsohon ministan babban birnin tarayya, Muhammad Bello.
Tsohon Ministan Kwadago da Samar da ayyukan yi, Chris Ngige, Tsohuwar Ministar Agaji, Sadiya Farouq da Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya Hammed Ali suma sun raka shi.
A wani labarin kuma,Da Dumi-Dumi: An Rantsar da Tinubu,Shettima a matsayin shugaban kasar Najeriya da mataimakinsa
An rantsar da Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima a matsayin shugaban Kasa da mataimakinsa a ranar Litinin 29 ga watan Mayu a wani biki da aka gudanar a dandalin Eagle Square da ke babban birnin tarayya Abuja,Vanguard ta rawaito.
Babban mai shari’a na tarayya Olukayode Ariwoola ne ya rantsar da shugaban kasar da misalin karfe 10:40 na safe jim kadan bayan mataimakin shugaban kasar ya sha rantsawar kama aiki.