• About Us
  • Blog
  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana gabda fara ginin masana’antun Iskar Gas a Jihar
  • Home
Monday, March 20, 2023
  • Login
Dimokuradiyya
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
Dimokuradiyya
No Result
View All Result
Home Uncategorized

Shin yaushe ne Gwamnatin Najeriya za ta haramta almajirci?

Mustapha Haruna Dabai by Mustapha Haruna Dabai
June 22, 2019
in Uncategorized
Reading Time: 3 mins read
0 0
0
0
SHARES
3
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Batun da ya ja hankalin ‘yan Najeriya a karshen makonnan shi ne fadin da gwamnatin Shugaba Buhari ta yi cewa abin da ta sa a gaba shi ne hana almajirci a nan gaba.

A sanarwar da mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Juma’a, Shugaban ya ce sabanin yadda wasu kafafen watsa labarai suke yayatawa cewa gwamnati za ta haramta almajirci, gwamnatin ta Buhari tabbas za ta dauki wannan hukunci amma fa a nan kusa ba.

A ranar Alhamis ne dai Shugaba Buhari ya nanata aniyarsa na ganin dukkanin yara ‘yan Najeriya sun samu ilimin da ya dace da su, inda ya ce zai dauki matakan magance hana kananan yara zuwa makaranta.

Wannan batu ne ya janyo kafafen watsa labaran hasashen cewa gwamnatin za ta haramta almajirci.

A makon da ya gabata ne dai Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya fitar da alkaluman da ke nuna cewa kimanin kananan yara miliyan takwas ba sa makaranta a jihohi 10 na Najeriya.

Asusun ya kara da cewa yaran dukkaninsu daga jihohin arewa suke:

  • Bauchi
  • Niger
  • Katsina
  • Kano
  • Sokoto
  • Zamfara
  • Kebbi
  • Gombe
  • Adamawa
  • Taraba.

Ana ganin rahoton Asusun na UNICEF na daga cikin abubuwan da suka yi tasiri kan yunkurin daukar matakin da Shugaba Buhari ya ce zai yi wajen ganin an magance matsalar rashin karatun yara a kasar.

Me jihohi ke yi kan almajirci?

Za a iya cewa batun almajirci yana ci wa jihohin arewacin kasar tuwo a kwarya, ganin cewa duk lokacin da aka fito da wasu alkaluma da ke nuna koma-bayan karatun yara, jihohin ne ke kunyata.

A makon da ya gabata Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ja kunnen mahaifan da ke tura ‘ya’yansu almajirci ko kuma bara maimakon makaranta, inda har ya ba da umarnin a kama yaran da mahaifan nasu.

Shi ma Sarkin Kanon, Muhammadu Sanusi na biyu ya shaida wa ‘yan majalisar jihar da suka ziyarce shi a fadarsa, cewa zai aiko da kudurin doka da zai tilasta wa iyaye kai yaransu makarantun boko.

Da zarar majalisar ta amince da kudirin ya zama doka, to duk iyayen da aka samu da laifin kin aika yaransu makaranta za su gurfana ne a gaban kuliya.

Ko a baya ma dai jihar ta Kano ta yi dokokin hana bara da suka tanadi kama almajiri da malaminsu, amma har yanzu matsalar ba ta ragu ba maimakon haka ma ƙara gaba-gaba take yi.

An dai sha gudanar da bincike da nazarce-nazarce da dama gami da ba da shawarwari kan yadda za a magance matsalar bara, musamman a arewacin Najeriya.

A 2014 wani kwamitin wasu fitattun mutane da suka shafe wata takwas suna yi wa gwamnonin arewa nazari kan wasu matsaloli musamman na bara, sun gabatar da rahoto kan yadda za a magance su.

Sai dai sama da shekara biyar da mika wa gwamnonin wannan rahoto, za a iya cewa ba a ga sauyi ba.

Mene ne almajirci?

Yanayi ne da iyaye kan tura yaransu zuwa ga wani malami domin koyar da su karatun alkur’ani, a wurin da ake kira makarantar allo.

A mafi yawan lokaci malamin da yaran kan yin nesa da garuruwansu, inda suke zuwa wasu birane domin samun sukunin karatun.

Kusan za a iya cewa kadan ne daga cikin mahaifan yaran kan bai wa malamin abincin da yaran nasu za su ci a tsawon zaman da za su yi da shi.

Mafi yawancin yaran kan fita bara kan tituna da gidaje domin neman abin da za su ci da ma neman kudin bukatunsu na yau da kullum.

Previous Post

Wata Kotu, Ta Haramtawa Gwamnatin Jihar Kaduna Kafa Dokar Wa’azi

Next Post

Za mu shafe Iran daga duniya idan yaki za mu yi – Trump

Next Post

Za mu shafe Iran daga duniya idan yaki za mu yi - Trump

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result
Arabic Arabic English English French French Hausa Hausa
  • Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    2455 shares
    Share 982 Tweet 614
  • Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ƙazamin Rikici Ya Kaure Tsakanin Shugaban Ƙungiyar CAN Da Isa Ashiru Kudan

    1995 shares
    Share 798 Tweet 499
  • Sai na yi lalata da kai na kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa sannan zan taimaka maka, Wata mata ga saurayi

    1693 shares
    Share 677 Tweet 423
  • Ga Irinta Nan: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Ƙi Amsar Cikin Da Ya Ɗirka Mata

    1365 shares
    Share 546 Tweet 341
  • CBN Ya Sake Fitar Da Sabbin Bayani Kan Dawo Da Tsofaffin Takardun Kudin Naira

    1592 shares
    Share 637 Tweet 398
Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe

Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe

March 20, 2023
INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

March 20, 2023
PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

March 20, 2023
Bayan Faduwa A Zaben Sake Darewa Kujerar Sanata Nnamani Ya Bar PDP

Bayan Faduwa A Zaben Sake Darewa Kujerar Sanata Nnamani Ya Bar PDP

March 20, 2023
Mohammed Ya Sake Lashe Zaben Gwamna Karo Na Biyu A jihar Bauchi

Mohammed Ya Sake Lashe Zaben Gwamna Karo Na Biyu A jihar Bauchi

March 20, 2023
Da Dumi-Dumi: Ɗan Takarar APC Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Sakkwato

Da Dumi-Dumi: Ɗan Takarar APC Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Sakkwato

March 20, 2023
Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe
Labarai

Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe

March 20, 2023
INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato
Labarai

INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

March 20, 2023
PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu
Labarai

PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

March 20, 2023
Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe

Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe

March 20, 2023
INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

March 20, 2023
PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

March 20, 2023

Twitter

Archives

Recent Posts

  • Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe
  • INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato
  • PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

Quick Links

  • Tsaro
  • Siyasa
  • Labarai
  • Wasanni
  • Kasuwanci
  • Rikicin Duniya

Contact Us

info@dimokuradiyya.com.ng

0809 912 4425 +234 809 912 4425

No. 218 Mogadishu layout Kaduna City Center Ahmadu Bello way kaduna. Kaduna, Nigeria 800273

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In