Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, ta sha alwashin cigaba da gudanar da gangamin da ta shirya yi a fadin kasar a ranar Alhamis, duk da sanarwar da gwamnatin tarayya ta yi na cewa ba za ta sake cire tallafin man fetur ba a yanzu.
Mataimakin shugaban NLC, Joe Ajaero, a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a shirin Sunrise Daily, ya bayyana cewa taron na da nufin wayar da kan ‘yan Najeriya.
“Har yanzu NLC na tsaye a kan matsayinta,” in ji shi a ranar Talata. “Gwamnatin tarayya ba ta ce ta soke ta ba, sun jingine ranar.
“Abun da muke yi shi ne wayar da kan ‘yan Najeriya game da wannan tallafin man fetur ko kuma abun da ake kira karin farashin man fetur.”
Shugaban kungiyar ya kara bayyana dalilan wayar da kan jama’a, inda ya ce cire tallafin man fetur na kara janyo wa ‘yan Najeriya wahala.
“Kungiyar NLC tana wayar da kan ‘yan Najeriya cewa hakan ba zai dore ba; cewa maganar tallafin man fetur karya ce da suke amfani da ita wajen jawo wa ‘yan Najeriya radadi.
“Don haka, taron da muka shirya ya nan. A ranar 27 ga Janairu, 2022, mun yi gangami a fadin kasar nan, ciki har da babban birnin tarayya Abuja,” in ji shi.
Ajaero ya bayar da hujjar cewa taron ya zama dole don fadakar da mambobin NLC kan hauhawar farashin man fetur da sauran kayayyakin da aka samu a duk shekara.
“Muna bukatar mu sanya dakarunmu a cikin shirin ko ta kwana kan duk wani mataki da za a dauka kan wannan batu na karin farashin man fetur daga farashin da ake sayar da shi zuwa sama da Naira 300 kan kowace lita,” ya jaddada.
A baya dai gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da shirin cire tallafin man fetur.
Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, a ranar Litinin ta ce gwamnati ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur.
Ta bayyana cewa gwamnati za ta yi tanadin tallafin man fetur fiye da wa’adin farko na watan Yuni a kasafin kudin 2022.