Daga: Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari na cikin wata ganawa da wakilan wadanda harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su.
An kai harin ta’addanci kan jirgin ne a ranar 28 ga watan Maris, 2022.
KARANTA WANNAN LABARIN: Takaita Zirga-zirgar Adai-daita Sahu Ya Rage Fashi Da Sauran Aikata Laifuka A Kano – Shugaban KAROTA
A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, fadar shugaban kasar ta ce, “Shugaba #MBuhari yana ganawa da wakilan wadanda aka sace a jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna.”
‘Yan ta’addan dai sun yi ta sakin wadanda abin ya rutsa da su a rukuni rukuni.
Jaridar PUNCH ta ruwaito a ranar Larabar da ta gabata cewa, ‘yan ta’addan sun sake sako wasu mutane bakwai da suka yi garkuwa da su, da suka hada da iyali guda shida da mace daya.
Asalin dangin su shida wadanda suka hadar da wani Uba, Abdubakar Garba; matarsa, Maryam; da dansu mai shekaru 10, Ibrahim; Fatima (7); Imran (5); da Zainab mai shekara daya da rabi.
Garba wanda ma’aikaci ne a hukumar yi wa ‘yan majalissar tarayya hidima, dan tsohon shugaban mulkin soja ne a jihohin Kano da Binuwai.
Haka kuma an saki wata mata mai suna Aisha Hassan mai shekaru 60 da haihuwa, wadda aka ce an sake ta ne sakamakon kalubalen kiwon lafiya da ke barazana ga rayuwa da ta tabarbare a baya-bayan nan.
A ranar 26 ga watan Yuli, 2022, jaridar Dimokuradiyya ta bayar da rahoton cewa, Gwamnatin Tarayya ta ba da tabbacin cewa, sakin fasinjojin da ‘yan ta’adda ke ci gaba da tsare su shi ne abin da suka sa a gaba.
Ministan Sufuri Mu’azu Sambo ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga iyalan wadanda abin ya shafa, wadanda suka jagoranci zanga-zangar lumana zuwa ma’aikatar domin neman a sako ‘yan uwansu.
“Gwamnati ba ta yi barci ba daga tambayoyin da na yi. Akwai wasu abubuwa da ba za mu fada a bainar jama’a ba, amma ina so ku ba ni lokaci,” in ji Ministan cikin wata sanarwa da ma’aikatar sufuri ta fitar a Abuja.
Ya kara da cewa, “Bari na koma yadda ya kamata a wannan ofishi kuma na yi muku alkawari, wannan shi ne batu na farko da zan tunkara da yardar Allah.
Sambo ya bukaci lambobin sadarwa, sunaye, adireshi, da lambobin wayar da zai iya samu, inda ya yi alkawarin cewa zai ci gaba da kasancewa tare da shi har sai duk wanda aka kama sun samu ‘yancin sake haduwa da iyalansa.