Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Madina na kasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki ta kwanaki takwas, Vanguard ta rawaito.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce da isar sa, mataimakin gwamna Sa’ud Khalid Al-Faisal ne ya tarbe shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Zai Tafi Saudiyya, Bayan Bukatar Gaggawa Ta Taso Masa
Kakakin shugaban kasar ya ce shugaban ya kai ziyara tare da yin addu’a a masallacin Annabi Muhammad mai alfarma.
Shehu ya kara da cewa a kofar masallacin Annabi mai alfarma, shugaban ya samu tarba daga jami’ai da dama.
A wani labarin kuma, Wata Mace Ta Shiga Takarar Gwamnan Jihar Kogi
Dokta Atule Ahmadu-Avolabi, wacce ta kasance ‘yar takarar mace a ranar Laraba ta shiga takarar gwamnan jihar Kogi a watan Nuwamba a karkashin jam’iyyar Labour Party (LP).
Dakta Ahmadu-Afolabi,wanda ta kasance likita ce ta shaida wa manema labarai hakan jim kadan bayan ta karbi fom din takararta a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja, inda ta ce ta mayar da hankali ne wajen yin amfani da karfin tattalin arzikin jihar.
“Babban abin da nake mayar da hankali a kai shi ne in tabbatar da cewa Kogi tana da karfin tattalin arziki ta hanyar ayyukan sadaukar da kai kuma jam’iyyar Labour kamar yadda muka sani jam’iyya ce ta zamantakewar dimokaradiyya.
“Jam’iyyar na dauke da kwararru, mata manoma da kowa da kowa, don tabbatar da cewa akwai abincin da za mu ci.
A jihar Kogi a halin yanzu, idan kana zagayawa jihar za ka ga yunwa a zahiri a fuskar mutane kuma hakan ya canza, shi ya sa na zo don in canza labarin da kyau.