Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa (NCTC), cibiyar da ya ayyana za ta zama babbar jigo ga gwamnati mai jiran gado domin yakan ayyukan ta’addanci. Kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Talata a yayin kaddamar da wasu kayayakin zamani guda biyu da suka hada da sabon ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a Abuja, a wani bangare na kokarin magance kalubalen rashin tsaro da ya ki ci yaki cinyewa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nafi Kowa Cancantar Zama Shugaban Majalisar Dattawa ta 10 – Barau
Da yake jawabi a wajen kaddamar da wasu manyan kayyakin, Shugaban ya bayyana cewa gwamnatinsa ta binciki masu tayar da kayar baya a yankin Kudu maso Gabas da ma yankin Kudu maso Yamma da ke son ballewa daga Najeriya
Kazalika ya ce, cibiyar zata magance matsalar satar danyen mai, fashin teku, satar fasaha, da tsagerun dake yankin Kudu-maso-Kudu.
Yayin da yake tsokaci kan barazanar dake fuskantar shafukan yanar gizon Najeriya, Shugaba Buhari ya jaddada alfanun kare sararin samaniyar kasar nan daga kowani irin nau’in farmaki.
A wani labarin kuma, Wani Sanata A Kudu Ya Bi Sahun Kalu Wajan Neman Kakakin Majalissar Dattijai
Zababben Sanata mai wakiltar mazabar Ebonyi ta Kudu, Dave Umahi ya bi sahun sauran Sanatocin da ke fafutukar neman kujerar Shugaban Majalisar Dattawa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Mataimaki na musamman ga Umahi kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Francis Nwaze ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Laraba.