Shugaban kasa, Muhammadu Buhari , a ranar Juma’a, ya bukaci majalisar dattawa ta tabbatar da nadin mutane 12 da aka nada a matsayin mambobin kwamitin gudanarwa na hukumar raya yankin arewa maso gabas.
A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, bukatar Buhari na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan mai kwanan wata 3 ga watan Mayu, 2023,Punch ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2022: An Farmaki ‘Yan Jarida 66 da Gidajen Yada Labarai 3 – IPC
Wasikar ta kara da cewa, ”A bisa tanadin sashe na 1, sashe na 2(5)(b) na dokar kafa hukumar raya yankin arewa maso gabas, ta shekarar 2017.
“Na ji dadin gabatarwa da majalisar dattawa domin tabbatar da nadin mutane goma sha biyu. 12) wadanda aka zaba kamar yadda aka nuna a kasa, a cikin Kwamitin Gudanarwa na Hukumar Raya yankin Arewa maso Gabas.
‘’Ana gayyatar majalisar dattawa da ta lura cewa wa’adin gudanarwar hukumar raya yankin arewa maso gabas zai kare ne a ranar 7 ga watan Mayu, 2023.’’
Wadanda aka nada sun hada da: Barista Bashir Baale shugaba, (Arewa maso gabas Yobe), Suwaiba Baba, babbar daraktar harkokin jinkai, (Arewa maso gabas Taraba), Musa Yashi, babban daraktan, gudanar da mulki da harkokin kudi (Arewa maso gabas Bauchi), Dr Ismaila Maksha, Babban Daraktan Ayyuka (Arewa maso Gabas, Adamawa) da Umar Hashidu, MD/CEO, (Arewa maso Gabas Gombe).
Sauran sune Grema Ali, mamba, (Arewa maso gabas Borno), Onyeka Gospel-Tony, mamba, (kudu maso gabas), Mrs Hailmary Aipoh mamba, (kudu maso kudu), Air Commodore Babatunde Akanbi (mai ritaya) mamba (Kudu maso Yamma).
Sannan akwai Mustapha Ibrahim, mamba, (Arewa maso yamma), Hadiza Maina, mamba, (Arewa ta Tsakiya) da wakili daga ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa.
Buhari ya bayyana fatansa na cewa bukatarsa ‘’zata samu karbuwa cikin gaggawa da kuma tabbatarwar majalisar dattawa’’.
Hukumar ta NEDC tana tantancewa, daidaitawa, da bayar da rahoton duk shirye-shirye da tsare-tsare na Gwamnatin Tarayya ko ma’aikatunta da Hukumomi, Jihohi; da sauran Abokan Ci Gaba da aiwatar da dukkan shirye-shirye da tsare-tsare na jihohin Arewa maso Gabas wato Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba, Yobe.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa a ranar 9 ga watan Mayun shekarar 2019, shugaban kasa ya kaddamar da sabbin shugabannin hukumar. Sai dai kuma a watan Maris din shekarar 2023, wasu kungiyoyin fafutuka biyu da na farar hula sun zargi Manajan Daraktan ta Mohammed Alkali da karkatar da kudaden kasafin kudin da ya kai Naira Biliyan N146.19bn.
A wani labarin kuma, Cire Sassan Jiki: Da Yiwuwar Sarki Charles Ya Yafewa Ekweremadu – Lauya
A yayin bikin nadin sarautar sabon sarkin Burtaniya da aka shirya yi a gobe Asabar, Sarki Charles III na iya yin afuwa ga tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, a cewar wani lauya Kayode Ajulo.
Ajulo ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a.