Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyya ga iyalan tsohon Atoni Janar kuma ministan shari’a, Prince Bola Ajibola, SAN, wanda ya rasu yana da shekaru 89 a duniya.
A lokacin da yake jajanta wa kungiyoyin lauyoyi a Najeriya da ma duniya baki daya, shugaba Buhari ya bayyana cewa fitaccen lauyan ya yi amfani da ilimi da basirar da Allah ya ba shi wajen tabbatar da adalci da gaskiya da daidaito a dukkan ayyukansa a ciki da wajen Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Antoni Janar Na Najeriya Bola Ajibola Ya Rasu
Shahararren mai sasantawa ya kasance a lokuta daban-daban inda ya riki mukamai da dama, Shugaban Kungiyar Lauyoyin Najeriya daga shekarar (1984-1985), Shugaban Kungiyar Alkalai ta Duniya, Shugaban Kungiyar Manyan Lauyoyin Najeriya da Shugaban Kotun Gudanarwa na Bankin Duniya da sauran manyan nasarorin daya samu.
Shugaba Buhari ya ce, Marigayi Ajibola, bayan ya kai ga kololuwar sana’arsa, ya kai hazakarsa ta fuskar shari’a zuwa kotun kasa da kasa da ke Hague, inda ya yi aiki nagari a tsakanin shekarar 1991-1994. Ya kuma kasance jakadan Najeriya a fannin shari’a a kasar Burtaniya daga shekarar 1999 zuwa 2002.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya fitar, ta rawaito Buhari na cewa, “Ba za a iya misalta gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban tsarin shari’armu ba, inda ya yi aiki a matsayin babban lauya kuma ministan shari’a a wani mawuyacin hali a cikin tarihin kasar. Kishin kasa, mutuncinsa da kishin hidima da ci gaban bil’adama za su ci gaba da dawwama a bayansa.”
Shugaba Buhari ya kuma jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Ogun a yayin da suke jajanta wa hazikin dan kasa kan ci gaban ilimi da zamantakewa da ya kawo wa al’ummarsa da muhallinsa.
Ya yi addu’ar Allah ya saka masa da Aljannah.
A wani labarin kuma,Mutuwar Hajiya Rabi Aminu Dantata, Rashi Ne Ga Kowa – Ganduje
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya bayyana marigayiya Rabi Aminu Dantata, matar hamshakin dan kasuwa kuma dattijon kasa, Aminu Alhassan Dantata, a matsayin uwa mai tarin dukiya, fitilar fata kuma uwa mai tarbiyya wacce ta siffata mutane da dama a kusa da ita zama masu albarka da adalci.
Ganduje ya bayyana haka ne a cikin sakon ta’aziyya da babban sakataren yada labaran sa, Abba Anwar ya aikewa dattijon kasa da daukacin iyalan Dantata bisa rasuwar matarsa.