Shugaban kasa Muhammadu Buhari a gobe Laraba zai tashi zuwa birnin Bissau na kasar Guinea Bissau wanda za a yi masa ado da babbar lambar yabo ta kasar sakamakon irin gudunmawar da ya bayar wajen tabbatar da dorewar siyasar kasar da ke yammacin Afirka.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Talata ta hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Gudun Hijirar Benue Za Su Kada Kuri’a A Zaben 2023 – INEC
Buhari zai amsa goron gayyatar da shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissolo Embalo ya yi masa na bikin na musamman a fadar shugaban kasa, wanda zai hada da kaddamar da wata hanya mai sunan sa a babban birnin kasar.
Bikin na kwana guda zai bayyana irin rawar da Buhari ya taka a gabar tekun Yamma, musamman a kasar Guinea Bissau, da nasiha da karfafa gwiwar shugabanni akai-akai kan kyawawan dabi’u na zaman lafiya, hada kai da siyasa, daidaito da kuma karfafa tattalin arziki mai karfi da zai samar da ci gaban kasa baki daya.
A ziyarar ta Bissau, Buhari da tawagar Najeriya za su halarci taron kasashen biyu.
Shugaban zai samu rakiyar karamin ministan harkokin wajen kasar Ambasada Zubairu Dada, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Mohammed B. Monguno (mai ritaya) da Darakta Janar na hukumar leken asiri ta kasa Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.
A wani labarin kuma, Dalilin Da Ya Sa Cin Hanci Da Rashawa Ke Kara Tabarbarewa A Najeriya – Jonathan
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a kasar nan domin “mutane ba su san abin da zai faru gobe ba.”
Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a matsayin babban bako na musamman a wajen bikin cika shekaru 73, da kaddamar da cibiyar kula da tsofaffi da kuma wani littafi na karrama tsohon shugaban majalisar dokokin jiha, Obioma Onwuzurumba, a Abuja ranar Talata.
Yayin da yake yabawa mai bikin tare da matarsa bisa shirin kaddamar da cibiyar kula da tsofaffi, tsohon shugaban ya koka kan rashin kula da ma’aikatan gwamnati, wadanda ya ce ba a bar su su mallaki sana’o’i ba, kuma har yanzu ba a kula da su. bayan lokacin hidimarsu.