By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a yau (Litinin) zai tashi zuwa birnin Riyadh na kasar Saudi Arabia, don halartar taron saka hannun jari da Cibiyar Inshorar zuba jari ta shirya.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana hakan a ranar Lahadi a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Shugaba Buhari zai halarci taron zuba jari a Riyadh, Saudi Arabia’.
Shugabannin za su kasance tare da shi a karo na 5 na babban taron saka hannun jari na manyan kamfanoni daga Najeriya, masu banki, shugabannin masana’antu da masana makamashin don tattauna batutuwan da za su shafi makomar saka hannun jari a fadin duniya.
Taron na kwanaki uku, mai taken: ‘Zuba Jari ga Dan Adam’, wanda zai karbi bakuncin shuwagabannin duniya da manajojin kadarori, za su bada shwarwari kan ci gaba da wadata da makamashi; iyakokin gaskiya na ƙarshe a cikin saka hannun jari, kimiyya a aikace, da tasirin canjin yanayi kan al’ummomi, da sauransu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa shugaba Buhari zai yi aikin hajji na umra a Madina da Makka kafin ya dawo kasar a ranar Juma’a, a cewar Shehu.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani, Dakta Isa Pantami ne zai yi masa rakiya, sai Karamin ministan harkokin waje, Zubairu Dada; Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva; Mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Manjo Babagana Monguno (mai ritaya); Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ahmed Abubakar; Manajan Darakta, Hukumar Zuba Jari ta Najeriya, Uche Orji, sai kuma Shugabar, Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.
Kazalika Wasu daga cikin sauran mahalarta daga kamfanoni masu zaman kansu a wannan tafiya sune Mohammed Indimi, Aliko Dangote, Tope Shonubi, Wale Tinubu, Abdulsamad Rabiu, Hassan Usman, Omoboyode Olusanya, Abubakar Suleiman, Herbert Wigwe da Leo Ekeh.