Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu yana ganawa da sarakunan gargajiya da wakilansu daga sassan kasar nan a yanzu haka a babban dakin taro na fadar shugaban Kasa da ke Aso Rock Villa A Abuja.
DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Taron wanda ake gudanar da shi a ranar Juma’ar nan wani bangare ne na wasu tsare-tsare da shugaban Kasar ke yi da masu ruwa da tsaki tsakanin masu zartarwa, ‘yan majalisa’ yan kasuwa da masu mukaman gargajiya tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan mayun bana.
KARANTA WANNAN Sarakunan Gargajiya Sun Rubutawa Tinubu Wasika
Taron wanda ake gudanar da shi a sirri, ana sa ran Tinubu zai tattauna batutuwan da suka shafi samar da waraka da hadin kan Kasa: kamar yadda ya yi bayani a jawabinsa na rantsuwa.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa A jawabinsa na bude taron, mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III wanda ya jagoranci takwarorinsa wajen taron, ya ce sarajunan sun ziyarci shugaban Kasar ne domjn taya shi murna tare da tabbata masa da goyan bayansu a kan aikin da ya ke yi na gini Kasa.
Sarkin Musulmim ya bayyana cewa majalisar sarakuna gargajiya tana da kwararru daga bangarori daban-daban, yada Tinubu zai iya amfani da somu wajen dora Nigeria kan turbar ci gaba.
Ya kuma bayyana cewa za su bashi goyan baya don ya daidaita ajandar manufofinsa masu kyau a Kasar.
A nasa jawabin Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Adewusi, ya bukaci shugaban Kasa Tinubu da ya yi “amfani” da sarakunan gargajiya wajen magance matsalar rashin tsaro.
“Mista Shugaban Kasa yi amfani da Mu. Yi amfani da Mu. Yi amfani da Mu,” in ji sarkin.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Daga cikin mahalarta taron akwai mataimakin shugaban Kasa Kashim Shettima; Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume; Babban Sakataren gidan gwamnati, Tijjani Umar; Sarkin Kano, Obi na Onitsha, Tor Tiv, Etsu Nupe, Deji na Ikare, Shehun Borno, Elegushi na Ikate, Jaja na Opobo, Lamidon Adamawa, Sarkin Zazzau, Gbong Gwom Jos, Attah Igala, Alake na Egbaland, da wakilin Oba na Benin.
A Wani Labarin Kuma EFCC Ta Kame Mutane 52 Da Ake Zargi Da Damfara Ta Yanar Gizo
Hukumar EFCC ta kame wasu mutane 52 da ake zargi da damfarar yanar gizo a jihar Ogun.
An kama wadanda ake zargin ne a wani samame biyo bayan bayanan sirri da hukumar ta samu kan ayyukan masu damfara ta yanar gizo.