Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya musanta cewa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Mahmood Yakubu yayi aiki a karkashinsa a ma’aikatar ilimi ta tarayya, kamar yadda Daily Post ta rawaito.
Wike ya ce shi da Yakubu sun yi aiki a ma’aikatar ilimi ta tarayya karkashin kulawar ministan ilimi.
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP Ta Yi Watsi Da Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Kaduna
“Amaechi ya yi kakkausar suka a cikin hirarsa ta baya-bayan nan cewa Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya gudanar da zabe mafi muni a tarihin Najeriya.
Wike “Ya kara da cewa (Amaechi) ya yi zargin cewa Mahmood Yakubu ya yi aiki a karkashina a matsayina na Minista kuma ya yi ikirarin cewa ya ki amincewa da sake nada shi ne saboda wani a sansanin zababben shugaban kasa na jam’iyyar APC ne ya zabe shi.
“Gaskiya Mahmood Yakubu bai taba yin aiki a karkashina ba. Mu biyu mun yi aiki a ma’aikatar ilimi ta tarayya. Ya kasance Babban Sakatare na Asusun Tallafawa Manyan Makarantu, wanda Ministan Ilimi ke kula da shi, a lokacin da nake Karamin Ministan Ilimi.
“Shin ba Mahmood Yakubu ba ne ya gudanar da zaben shekarar 2019, wanda APC da Shugaba Muhammadu Buhari suka yi nasara?”
A wani labarin kuma,INEC Ta Musanta Zargin Murde Sakamakon Zaben Wata Jiha
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta karyata wani rahoto da ke zargin shugabanta Farfesa Mahmood Yakubu, na yunkurin murde sakamakon zaben gwamna a jihar Abia.
Wani shafin yanar gizo mai suna Strenuous Blog, ya ruwaito jami’ar dake kula da tattara sakamakon zaben ta Abia, Nnenna Oti, tana zargin an tilasta mata yin abin da bai dace ba.