Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na mazaba ta 9, a karamar hukumar Warri ta Kudu a jihar Delta, Mista Vincent Okokoje ya fadi ya mutu.
Rahotanni sun ce ya rasu ne a safiyar ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sudan: Buhari Yayi Kiran A Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Bangarorin Dake Fada da Juma
Shugaban Jam’iyyar APC na mazaba ta 12, Kwamared Gabriel Omorere ya tabbatar wa DAILY POST rahoton rashin.
Ya ce, “mun halarci wani taro a gidan wani jigo a jam’iyyar APC a yankin Warri ta Kudu, Cif Ojogri a ranar Laraba da ke kan hanyar Warri/Sapele. Mun samu labarin cewa ya rasu ne da safiyar Alhamis.”
Omorere ya ce mutuwar Okokoje ta zo wa jam’iyyar APC a yankin Warri ta Kudu da kuma jihar Delta baki daya.
Ya ce marigayi Okokoje mutum ne mai son zaman lafiya a tsakanin abokan aikinsa.
A cewar Omorere, “Ya na daga cikin shugabannin unguwanni uku da suka lashe mazabarsu a zaben da aka kammala a mazabar Warri ta Kudu II.”
Omorere, wanda ya jagoranci tawagar shugabannin jam’iyyar APC a yankin Warri ta Kudu a ziyarar ta’aziyya ga uwargida, ‘ya’yansa da iyalan Okokoje, ya ce za a yi kewarsa matuka.
Ya jaddada cewa ficewar tasa bata haifar da da mai ido sosai a cikin jam’iyyar APC a yankin Warri ta Kudu ba, inda ya ce, “Ina rokon Allah ya ba mu wani irinsa da zai yi aiki tukuru domin ciyar da jam’iyyar gaba.
A wani labarin kuma, Rabo: Wani Matashi Mai Matsakaicin Shekaru Ya Lashe Zaben Kujerar Majalisar Wakilai
A daren Lahadi ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta bayyana Akarachi Amadi mai shekaru 29, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress APC, a matsayin wanda ya lashe zaben ciko na mazabar Mbaitoli/Ikeduru na jihar Imo a ranar Asabar,Punch ta rahoto.
Da yake bayyana kuri’un da aka kadawa ‘yan takarar a cibiyar tattara sakamakon zaben mazabar tarayya da ke Nworuibi a karamar hukumar Mbaitoli, jami’in zaben, Farfesa Boniface Okoro, ya ce dan takarar jam’iyyar APC ya samu mafi yawan kuri’u.