Shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin bude taron kasa karo na 3 kan rage cin hanci da rashawa a bangaren gwamnati, wanda hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC tare da hadin gwiwar ofishin sakataren gwamnatin tarayya suka shirya.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadin da ta gabata ta hannun mai magana da yawun hukumar ta ICPC, Azuka Ogugua.
Jaridar Dimukuradiyya ta ba da rahoton cewa taron mai taken ‘Cin hanci da rashawa da tsadar mulki: Sabbin Mahimmanci don gane Kuɗin haramun’ an shirya gudanar da shi ne a ranar 30 ga Nuwamba, 2021 a Cibiyar Taro na Gidan Gwamnati (Old Banquet Hall), a Fadar gwamnati da ke Villa a Abuja.
” Za kuma a rika yada shirin kai tsaye a Shafin sada zumunta na a Facebook @ICPCNIGERIA.
Shugaba Buhari zai kuma aminewa jama’a tare da bai wa wasu ma’aikatan gwamnati guda biyu da suka yi fice da ayyukan gaskiya lambar yabo ta 2021, yayin da wani dan kasa mai zaman kansa za a amince da shi a matsayin Alamar kungiyar sa kai ta ‘yan kasa da ke yaki da cin hanci da rashawa,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce, manyan mutane da ake sa ran za su gabatar da jawabai a wajen taron da ke mai da hankali kan yaki da cin hanci da rashawa a bangaren gwamnati, su ne shugaban majalisar dattawa, Sanata Dr. Ahmad Ibrahim Lawan; Babban Alkalin Alkalan na Kasa, Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha. Mai girma ministar kudi, kasafin da tsare-tsare ta kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, za ta gabatar da jawabi mai taken: Cin hanci da rashawa da tsadar mulki; Sabbin Mahimmanci domin Fahimtar Kuɗin haramun.
Ya ce an shirya wasu masu fafutuka shida don tattauna batutuwan da suka shafi yaki da cin hanci da rashawa a wajen taron cikin fasaha. Sun hada da Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kudi na Tarayya, Ben Akabueze, wanda zai yi magana a kan cin hanci da rashawa da kuma tsadar mulki wajen daukar ma’aikata; Sakataren zartarwa na kwamitin shugaban kasa kan yaki da cin hanci da rashawa (PACAC), Farfesa Sadiq Radda, wanda zai yi magana a kan cin hanci da rashawa da kuma tsadar tafiyar da mulki a fannin tsaro, da kuma magatakardar hukumar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede, wanda zai yi magana ne kan rashawa da kuma tsadar mulki a bangaren ilimi. Sauran wadanda zasu yi magana a zaman cikin fasaha sun hada da Darakta-Janar na kungiyar gwamnonin Najeriya, Mista Asishana Okauru; da Mista Hafiz Mohammed na hukumar ICPC.
“Ana sa ran za su yi magana a kan cin hanci da rashawa da kuma tsadar mulki a matakin kananan hukumomi, cin hanci da rashawa da kuma tsadar mulki a bangaren lafiya, da kuma almundahana da tsadar mulki wajen gudanar da ayyukan gwamnati. Duk zasu zo ne ta hanyar gayyata kuma duk mahalarta za su zauna da karfe 9.30 na safe.”
Comments 1