By Ishaq Dabai
Gwamnan lmo Hope Uzodinma yace shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar a ranar Talata 9 gawatan Satumba.
Gwamnan ya bayyana hakanne yayin da yake zan tawa da manema labarai a filin jirgin sama na Sam Mbakwe dake Owerri a yau Asabar.
Uzodinma wanda ya fadi hakan yayin dawowarsa daga birnin tarayya Abuja yace shugaban kasa da sauran hukumomin zasu yi aiki tare dan ciyar da gwamnatin gaba.
Gwamnan yace yakai ziyar Abuja “dan magance al’amuran siyasa da sauran wasu batutuwa wadanda ake zaton kula dasu a Abuja”.
Ya saurari batutuwa daga gwamnatin tarayya na shirin tallafin Bankin duniya na ginawa kauyuka tituna, da shirin gina muhalli da ma’aikatar kula da girgizar kasa NEWMAP da sauran masu kula da girguzar kasa.
Anasa jawabin shugaban jam’iyar APC na jihar Anambara da mai yakin neman zaben gwamna, Uzodinma ya kara da cewa sune suke da alhakin kula da jam’iya bisa gaskiya duba da muhimmancin ta.
Gwamnan ya bada tabbacin cewa suna aiki matuka wajen isar da sako ga mutanen jihar dasu tashi su sake zabar jam’iyar APC a zaben da za’ayi na 6 gawatan nuwanba.