- Shugaban kasa Tinubu ya nada Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa a yau, 2 ga watan Yuni, 2023.
- Gbajabiamila dai ya shafe shekaru dai dai har 20 da suka gabata a majalisar dokokin Najeriya.
- Kakakin majalisar mai barin gado yace zai yi iyakacin kokarinsa don ganin ya sauke aikin da ke gabansa cikin himma.
Bayan nadin da ya yi masa a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a yau, 2 ga watan Yuni, 2023, kakakin majalisar wakilai mai barin gado, Femi Gbajabiamila, ya baiwa shugaban kasar tabbacin kwazonsa da biyayyarsa ga wannan aiki.
Dan majalisar ya bayyana hakan ne a wani sakon godiya da ya aikewa shugaban a shafin Twitter bayan bayyana nadin nasa.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Anyanka Ta Tashi:Kungiyar NLC Za Ta Tsunduma Yajin Aikin Gama Gari
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Tinubu ya kuma nada tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa Sen. Ibrahim Hadejia, a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata kuma tsohon ministan ayyuka na musamman, George Akume, a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Gbajabiamila, wanda ya shafe shekaru ashirin da suka gabata a majalisar dokokin Najeriya, ya bayyana matukar godiya ga shugaban da ya dauko shi kuma yaga ya cancanci nadin.
Da yake yin mubayi’a ga shugaban kasa, sabon shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa zai yi iyakacin kokarinsa don ganin ya sauke aikin da ke gabansa cikin himma.
Ya rubuta, “Na gode Mista Shugaban kasa, Bola Tinubu, saboda ganin na cancanci zama shugaban ma’aikatan ku.
“Bayan shafe shekaru 20 da suka gabata a majalisar dokokin Najeriya, kuma bayan lashe zabena karo na 6 na zama ‘yan majalisar tarayya, zan yi aiki tare da shugaban kasa.
“Zan ba da mafi kyawuna lokacin da na shiga ofis a ranar 14 ga watan Yuni 2023 kamar yadda aka nuna a cikin Wasikar shugaban kasa.”
A wani labarin kuma, Wani Kakakin Majalisar Dokoki Ya Musanta Yin Murabus, Yace Wasikar Ta Karyace
Kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, Mista Bamidele Oloyeloogun ya musanta yin murabus.
Oloyeloogun yace wasikar ta karya ce ba ta fito daga gare shi ko kuma daga majalisar ba.
Kakakin majalisar yace ‘Na kasance shugaban majalisar dokokin jihar Ondo har yanzu.’