Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano Alhaji Shehu Wada Sagagi ya nemi shugaban jam’iyyar na ƙasa Iyorchia Ayu da ya gaggauta ajiye muƙaminsa na shugaban jam’iyyar .
Sagagi ya bayyana hakan ne a yammacin ranar Talatar nan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Kano, a Shalkwatar jam’iyyar ta jihar ?.
Ya ce Ayo yayi alƙawarin cewa zai yi murabus idan aka tsayar da ɗan arewa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa domin baiwa al’ummar yankin Kudu dama.
“To yanzu an tsayar da ɗan Arewa ya kamata ya mutunta wannan yarjejeniya, saboda su ma jama’ar kudu su samu nutsuwar zaɓar mu”.
Ya ƙara da cewa “Ɗan takarar shugaban ƙasa daga Arewa, shugaban jam’iyya daga Arewa, shugaban kwamitin amintattun jam’iyya shi ma daga Arewa, Shugaban gwamnonin jam’iyya shima daga Arewa, ci gaba da tafiya a hakan ba adalci ba ne ga ƴan kudu”.
Ya ce, shugabannin jam’iyyar PDP na Kano sun jaddada mubaya’a da biyayyarsu ga jam’iyyar PDP.
Ya ƙara da cewa, sun yi shirin tallata ɗan takarar jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da sauran waɗanda jam’iyyar ta tsayar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Dangane da ɓarakar da jam’iyyar ke fama da shi ya ce, suna cigaba da tattaunawa domin neman haɗin kan sauran ƴaƴan jam’iyyar.