Shugaban jam’iyyar PDP a babban birnin tarayya Abuja, Sunday Zakka ya rasu a wani hatsarin mota.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Zakka, an ce ya mutu ne tare da direbansa da direba a wani hatsarin mota.
KU KARANTA KUMA APC na tada tarzoma ne don a ɗage zaɓen Najeriya – Inji Atiku
Sakataren jam’iyyar PDP na babban birnin tarayya, Bako Angulu ya tabbatar da rasuwar a safiyar ranar Asabar.
Ya ce, Zakka tare da direbansa da direba sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe zuwa Kuje Road, da ke Abuja a daren ranar Juma’a.
Zakka na kan hanyarsa ta zuwa Kuje, garinsu, a shirye-shiryen zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi a yau a lokacin da hatsarin ya afku.
A Wani Labarin Kuma BVAS Ta Kasa Tantance Wike Da Matarsa
Gwamna Nyesom Wike na Ribas ya ji takaici a mazabarsa mai suna Ward 9, Unit 7, karamar hukumar Obio/Akpo a ranar Asabar, yayin da BVS ta kasa ba shi damar kada kuri’arsa.
BVAS ta kasa gane babban yatsan hannu ko fuskar matar sa, Suzzet Wike yayin da mai kula da Na’ura Agatha Abiokun yazo ya gyara amma ta gasa gane shi.