Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce ’yan siyasa da ke sayen katin zabe na dindindin (PVCs) don murde zaben 2023 na yin wani yunkuri ne na banza. Kamar yadda Channels TV ta ruwaiti.
A cewar INEC, Na’urar BVAS, fasahar da za a yi amfani da ita wajen tantance masu kada kuri’a a shekarar 2023, za ta ki amsan bayanan mutanen da ba su keda asalin katin zaben na dindin ba wato PVC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masu Adawa Da Dimokaradiyya Na Iya Yin Zagon Kasa A Zaben 2023, Falana Ya Ja Hankali
Wasu kungiyoyi masu zaman kansu guda biyu, da suka hadar da kungiyar dattawan Arewa da kungiyar kare hakkin jama’a da tabbatar da mulki na gari, sun yi zargin cewa ‘yan siyasa na sayen katin zabe daga talakawan masu kada kuri’a domin yin magudi a zabe mai zuwa.
Sai dai Okoye a ranar Lahadin, ya bayyana siyan katin zaben amatsayin abun da “ba zai yi tasiri ba”.
Ya dage cewa, Laifine a sami wani da katin zaben dindindi wato PVC wanda ba daya ba, yana mai cewa jami’an tsaro ne ke da alhakin bin irin wadannan mutane da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Tarayya Ta Fitar Da Hujjojin Tattaunawa Da Twitter Bayan Dakatar Da Ita
Gwamnatin Tarayya ta karyata zargin da wani tsohon ma’aikacin shafin Twitter ya yi cewa shafin yanar gizo na micro-blogger bai tattauna da gwamnatin Najeriya ba bayan dakatar da shi.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a ranar Litinin a Abuja wanda ya karyata wannan ikirari ga manema labarai, ya fitar da hujjojin tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnati da Twitter.
Ministar tya yi wannan jawabi ne a taro karo na 13 na bada maki a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a (2015-2023) wanda ya kunshi ministar harkokin mata, Paulen Tallen