Hedikwatar sojin Nijeriya ta ce rundunar sojin sama ta Operation Lafiya Dole na ci gaba da ragargaza maboyar ‘yan ta’adda tare da kashe da dama a maboyar ‘yan ta’adda biyu a jihar Borno.
Daraktan watsa labarai na Hedikwatar tsaron, Manjo Janar John Enenche ne ya tabbatar da hakan a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce an kai harin ne a ranar Asabar a Kote Kura da Bulama Isamari dake jihar Borno.
Manjo Janar John Enenche, ya ce sojin saman sun yi amfani da dabaru da kuma jiragen sama wajen kaddamar da hare-haren bisa rahotannin sirri da suka samu. Ya kara da cewa bayanan sirrin sun nuna cewa Boko Haram sun yi sansani a tsakanin wadansu garuruwa biyu inda suka ajiye kayayyakinsu da kuma shirin kaddamar da wadansu hare-hare.
Kote Kura dai na yankin Bama a yayin da Bulama Isamari yake tsakanin Timbuktu.