Dakarun hadin guiwar sojojin Najeriya da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun yi nasarar dakile wani harin da wasu da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka kaiwa Kano.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Brig.-Gen. Onyema Nwachukwu, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
Nwachukwu ya ce dakarun sojin Najeriya Birged 3 tare da hadin gwiwar hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun kai farmaki maboyar ‘yan ta’addan a safiyar ranar Juma’a a karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano.
Ya ce an gudanar da farmakin ne da nufin ganowa tare da damke ’yan ta’addan da ake zargin ‘yan Boko Haram ne da ake kyautata zaton suna shirin kai wani gagarumin farmaki a jihar.
Karanta nanMotocin N1.5bn Ba Don Amfanin Uwargidan Shugaban Kasa Ba Ne — Ndume
Saboda haka, sojojin sun yi gaggawar kai farmaki inda suka kama mutane biyu da ake zargi, wadanda yanzu haka suke tsare.
A yayin samamen, sojojin hadin gwiwa sun kwato bindigu kirar AK 47 guda biyar, jakar alburusan AK 47 guda biyar, bindigar roka daya (RPG da RPG Bombs guda biyar).
Sauran sun hada da Grenades na Hannu, nau’i-nau’i biyar na Desert Camouflage Uniforms, nau’i-nau’i na alburusai guda 10 da wasu kayan fashewar da aka inganta (IED)in ji shi.
Nwachukwu ya ce hadin gwiwa tsakanin rundunar sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro a matsayin misali wajen gudanar da aikin, shaida ne na irin karfin da suke da shi na ganin bayan ‘yan ta’adda da sauran kalubalen tsaro.
Ya kara da cewa wannan nasarar da rundunar ta samu ya karfafa jajircewar sojojin Najeriya na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
A wani labarin KumaGwamna Idris Ya Bukaci Hukumar FRSC Ta Kara Kaimi Wajen Rage Yawan Hadurra A Jahar Kebbi
Hukumar ta NA ta ci gaba da dagewa wajen ganin ta dakile da kuma kaskantar da ayyukan ta’addanci da sauran nau’o’in kalubalen tsaro a fadin kasar nan.
Muna kira ga jama’a da su yi taka tsantsan tare da hada kai da sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro ta hanyar samar da sahihin bayanai a kan lokaci da kuma sahihan bayanai wadanda za su taimaka wajen gudanar da ayyukan da ake yi na dakile rashin tsaro.
Rundunar Sojin Najeriya ta nanata sadaukarwarta wajen kare kasarmu da muke kauna kuma tana godiya da goyon baya da amincewar al’ummar Najeriya in ji shi.