Sojoji sun kama mutum 2 bisa laifin kashe wani Malami
Dakarun rundunar tsaro ta Operation Safe Haven (OPSH) da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Filato, da wasu sassa na jihohin Bauchi da Kaduna, sun cafke wasu mutane biyu bisa laifin kashe wani Malamin addini, Naman Stephen Ngophe.
Daily Trust ta ruwaito yadda wasu ‘yan bindiga suka kona gidan cocin Katolika da ke Kamanton a karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna a ranar 9 ga watan Satumba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Ikon Allah, za mu yi nasara a yaki da ƴan ta’adda
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar OPSH, kakakin rundunar, Captain Oya James, ya bayyana sunayen wadanda ake zargi da suka haɗa da Ahmed Abdullahi da Hassan Mato.
Amma da yake mayar da martani, Abdullahi ya musanta zargin, yana mai cewa bai san komai ba game da wannan laifi.
Ya ce, “Ina gida sai jami’an tsaro suka zo suka kama ni. An kawo ni nan aka hukunta ni mai tsanani ba tare da na aikata wani laifi ba. Ni daga gidan sarauta ne kuma ba zan iya yin irin wannan laifin ba. Ba a gaya mini abin da na yi ba sai yanzu.
A wani labarin kuma:Ƴancin bangaren shari’a ya jawo kayar da Tinubu a kotun Amurka – Phrank Shaibu
Phrank Shaibu, mataimaki na musamman kan hulda da jama’a ga Atiku Abubakar, ya ce ‘yanci kan harkokin shari’a na Amurka ne ya sa shugaba Bola Tinubu ya sha kaye a Kotun gundumar Illinois.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga umurnin da Mai Shari’a Nancy Maldonado ta bayar na cewa Jami’ar Jihar Chicago ta fitar da duk wani tarihin karatun Tinubu ga Atiku.