Hedikwatar tsaro a ranar Alhamis, ta ce dakarun Operation Hadarin Daji, a ranar 21 ga watan Mayu, sun kama wani dan kasar waje, Jabe Buba, kuma fitaccen dan ta’adda, a kauyen Garuwa, dake karamar hukumar Tambuwal a jihar Sokoto.
Manjo Janar kuma Daraktan ayyukan yada labarai na Ma’aikatar tsaro ta kasa Bernard Onyeuko ne, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan soji a fadin Najeriya, tsakanin 19 ga watan Mayu zuwa 2 ga watan Yuni a Abuja.
Onyeuko ya bayyana cewa an gano hotuna da bidiyo na Buba da bindigu a cikin dajin, da wayar salular sa kuma an karbo kudi naira 130,000 daga hannun sa a yayin farmakin.
A cewarsa, sojojin sun kuma kwato shanu 292 da rakumi daya a yayin wata arangama da ‘yan ta’adda a kauyen Dampo da ke karamar hukumar Bakura a jihar Zamfara.
Jami’an Operation Whirl Stroke ne su ka yi nasarar wannan harin.
Inda Kuma Onyeuko ya Kara da cewa, sojojin sun yi nasarar kashe wani shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane da kuma wasu mutane biyu wadanda dukkansu sanye da kakin soji suke a hanyar Zakibiam-Ugba a Binuwai tare da kubutar da wani da abin ya shafa.
Ya ce kayayyakin da aka kwato sun hada da mota kirar Toyota Corolla guda daya, da mujallu uku,, bindiga kirar AK 47 daya, da katin ATM mai dauke da sunan Felix Terzenqwe.
Onyeuko ya ce an kama wani fitaccen dan bindiga Mai suna, Mista Morris Ayitu tare da matarsa da wani abokinsa, bayan wani samame da suka kai gidansa da ke Abirisi a karamar hukumar Guma a jihar Nasarawa.