Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, a ranar Litinin, ya ce dakarun ‘Operation Forest Sanity’ sun kubutar da wasu mutane tara da aka yi garkuwa da su a yayin sintiri ga wasu da ake zargin ‘yan fashi ne a Kaso, cikin karamar hukumar Chikun ta jihar.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Kwamishinan, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Litinin, a Kaduna.
Sanarwar ta ce sojojin sun yi artabu da ‘yan bindiga a babban titin Tantatu, yayin da ‘yan bindigar suka yi bar sansaninsu suka gudu zuwa cikin daji.
KARANTA KUMA Jami’an Tsaro Sun Kubutar Da Mutane 76 a Jihar Kaduna
“Amma da ake binciken maboyarsu, ya ce mutane tara da aka yi garkuwa da su, ya bayyana sunayensu kamar haka Salama Oliver, Husseini Odu, Danjuma Jakanwa, Ezekiel Garba, Obadiah Moses, Taiwo Isaac, Buky Isaac, Ado Adamu, da Maigari Shekarau, kuma sojojin ne suka ceto su,” in ji sanarwar.
“Bayanin farko da aka yi wa wadanda aka ceto ya nuna cewa an yi garkuwa da su a kusa da yankin Dam Gurara,” in ji sanarwar.
Kwamishinan ya kara da cewa sojojin sun kuma kwato shanu 90 da ‘yan bindigar suka gudu suka bari.
“Za a mika dabbobin ga hukumar kula da kiwon dabbobi ta jihar Kaduna domin tantance su yadda ya kamata,” inji shi.
Ya ce an ci gaba da sintiri a tsaunin Bawa Rikasa inda aka samu nasarar kwato babura hudu na barayin.
“Mutanen tara da aka ceto za a ci gaba da tantance su kafin a sake haduwa da iyalansu. Za a ci gaba da sintiri na yaki a yankin baki daya,” in ji kwamishinan. Kamar yadda jaridar Solacebace ta rawaito
A Wani Labarin Kuma CBN Ya Baiwa Yan Bangaren Fito Tallafin Biliyan 81
Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya ce bankin ya biya kudi Naira biliyan 81 ga masu fito na Najeriya, domin bunkasa tattalin arzikin da ba na man fetur ba a kasar.
Emefiele ya bayyana hakan ne a yayin wani taron na RT-200 wanda aka gudanar a Legas, a Talatar nan.