Yawan mutanen muka rasa Isra’ila a harin ba-zata da Hamas ta kai ranar Asabar ya haura sama da 200, in ji rundunar sojin kasar, inda ta zargi mayakan Falasdinawa da kutsawa cikin gidaje da kuma kisan fararen hula.
Yan ta’adda sun kai farmaki tare da shiga gidaje, inda suka yi wa fararen hula kisan kiyashi in ji rundunar, inda ta kara da cewa sama da mutane 200 ne aka kashe tare da raunata fiye da 1,000 a harin da ya fara tun da asuba.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin daukar fansar abin da ya kira bakar rana ga Isra’ila, yana mai cewa sojojin za su mayar da martani ga kungiyar Hamas ta Falasdinawa da karfin tsiya.
Karanta nanGwamnatin Tarayya Ta Samarda Fili Mai Girman Hecta 70,000 Domin Noman Alkama
Rundunar sojin Isra’ila IDF na gab da yin amfani da dukkan karfinta wajen lalata karfin Hamas in ji Netanyahu a cikin wata ‘yar gajeriyar sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin.
Za mu kai musu hari har zuwa karshe kuma za mu dauki fansa da karfi a wannan bakar rana da suka yi wa Isra’ila da al’ummarta,” in ji shi, bayan da mayakan Hamas suka kaddamar da wani harin ba-zata, inda suka tura daruruwan mayaka cikin Isra’ila a karkashin wani katon roka.
Rikicin bindiga ya barke cikin dare bayan wani kazamin harin da Hamas ta kai wa Isra’ila a ranar Asabar, inda ta harba dubban rokoki daga Gaza tare da tura mayaka don kashe da kuma sace sojoji da fararen hula.
A wani labarin kumaBa Zamu Zura Ido Muna Kallon Hamas Ta Karar Da Isra’ila Ba-Netanhayu
Harin dai na nuni da irin wannan hari na farko da aka hada kai na kasa da iska da kuma ta ruwa, wanda ya kai rabin karni bayan barkewar yakin Larabawa da Isra’ila a shekara ta 1973.
Muna cikin yaki Netanyahu ya fada wa al’ummar da suka cika da mamaki yayin da sojoji suka mayar da martani ta hanyar kai hari a cikin shingen da aka katange, inda aka mayar da wasu gine-ginen hasumiya zuwa baragizai.