Dakarun runduna ta 26 wato Task Force Brigade, a ranar Talata, sun gano wata Misis Mary Ngoshe, wacce a cewar rundunar sojin Najeriya, tana daya daga cikin ‘yan matan da aka yi garkuwa da su a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke Chibok.
A shekarar 2014, ne dai yan ta’addan boko haramta, suka yi garkuwa da tarin yan mata dake makarantar sikandire Chibok, wadda ta mata ce zalla dake jihar Borno.
Matar wato Ngoshe, wadda aka same ta da wani yaro da ake kyautata zaton nata ne, sojojin sun tare ta ne a lokacin da suke sintiri a kewayen wajen dake a jihar Borno.
Hakan na kunshe ne a wani sako da aka wallafa a shafin Twitter na rundunar sojin Najeriya, @HQNigerianArmy, a safiyar Laraba.
Sanarwar ta ce, “Dakarun 26 Task Force Brigade da ke sintiri a kewayen Ngoshe a jihar Borno a ranar 14 ga watan Yuni 2022 sun kama wata Misis Mary Ngoshe da danta.
Kuma ana kyautata zaton tana daya daga cikin ‘yan matan da aka sace daga GGSS Chibok a shekarar 2014.
Har yanzu dai ana ci gaba da binciken matar domin tabbatar da samun wasu ƙarin bayanai.