Sojojin Nijar sun shirya tsaf domin tattaunawa
Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojan Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ya amince da lalubo hanyar tattaunawa ta diflomasiyya don warware rikicin siyasa a kasar.
Tchiani ya yi wannan jawabi ne a ranar Asabar, yayin wani taro da Tawagar Malamai daga Najeriya domin shiga tsakanin Ecowas da Shuwagabanni Mulkin Sojin kasar Niger karkashin jagorancin shugaban Kungiyar Izalah na kasa Sheikh Bala Lau.
A cewar wata sanarwa da Bala Lau ya sanya wa hannu a ranar Lahadin, Malamin ya shaida wa Tchiani cewa “ziyarar tasu zuwa Nijar na da manufar tattaunawa mai ma’ana don ƙarfafa shi da sauran shugabannin Sojojin da suka yi juyin mulki su rungumi tattaunawa maimakon yaƙi don warware rikicin.”
Da yake mayar da Jawabi, Tchiani ya ce, “kofofinsu a buɗe suke don bin
diflomasiyya da zaman lafiya wajen warware lamarin.”
Tchiani ya bayyana bakin cikinsa cewa Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ta Ecowas, ta basu wa’adi ne ba tare da jin ta bakin bangaren mulkin Sojin ba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Kano Ta Sake Bude Asibitin Yara Da Ganduje Ya Rufe
Mun samu labarin cewa Tchiani a ta bakin Firainistan Jamhuriyar Nijar Ali Zeine a shirye yake don tattaunawa tare da bayyana fatan ganin tattaunawar da kungiyar ta ECOWAS za ta gudana nan da ‘yan kwanaki kaɗan masu zuwa.
Zeine ya kara da cewa, “Mun amince, kuma shugaban kasarmu ya bayar da Kofar tattaunawa, tare da fatan cewa tawagar Malaman za su koma su sanar da shugaban Najeriya abin da suka ji daga gare mu, muna fatan nan da kwanaki masu zuwa su Ecowas za su zo nan domin tattauna gami da duba hanyoyin za a dage takunkumin da aka ƙaƙaba mana”.
A ranar Alhamis ne shugabannin kasashen yammacin Afirka suka kara zafafa kalamai kan shugabannin jamhuriyar Nijar da suka yi juyin mulki, inda suka ba da umarnin aike da dakarun Soji domin maido da mulkin dimokuradiyya a kasar.
Jamhuriyar Nijar dai ta fada cikin ruɗanin siyasa tun a karshen watan da ya gabata lokacin da aka hambarar da shugaba Mohamed Bazoum a wani juyin mulki da jami’an tsaron fadar shugaban kasar suka yi.
Kungiyar ECOWAS ta mayar da martani kwanaki ƙadan Bayan juyin Mulkin, gami da sanya takunkumi tare da ba da wa’adin wasu kwanaki ga gwamnatin mulkin soja da ta mayar da mulki ga Mohamed Bazoum ko kuma ta fuskanci fushin kungiyar.
Wannan wa’adin ya zo kuma ya tafi tun a ranar Lahadi 6 ga watan Agusta ba tare da an samu sauyi a harkokin siyasa ba, yayin da shugabannin ECOWAS suka jaddada buƙatar samar da hanyar diflomasiyya don warware rikicin, ko kuma su tura sojoji a matsayin mafita ta karshe.
A wani labarin kuma:“Ku kwantar da hankalin ku, Muna tare da ku” ~ Tinubu ya jaddada wa Matasan Najeriya
Shugaban ya ba da wannan tabbacin ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a dandalin Sadarwar shi na X wato wanda aka fi sani da Twitter a ranar Asabar don yin bikin murnar ranar matasa ta duniya ta shekarar 2023.
Tinubu ya yi nuni da cewa, al’ummar kasar suna goyon bayan Matasa yayin da suke fafutukar cimma burin su daban-daban.