Sojojin Ukraine sun ce sun harbo jiragen yaki guda biyar da wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakar kasar Rasha.
Hakan ya biyo bayan harin da aka kai a baya kan Ukraine bisa umarnin shugaban kasar Rasha Valdimir Putin.
Kakakin tsaron Ukraine ya ce akwai yiwuwar an kashe daruruwan sojojin Rasha a lamarin.
Hukumar tsaron kan iyaka ta Ukraine ta kuma ce sojojin Rasha sun kai hari kan kasar daga makwabciyarta Belarus.
Hukumar ta ce sojojin na Rasha sun yi luguden wuta da makami a wani bangare na harin da Belarus ke marawa baya.
“Ana kai hare-hare kan sassan kan iyaka, ma’aikatar tsaro da kuma shingayen binciken ababan hawa da manyan bindigogi da kuma kananan makamai. Har ila yau, an rubuta ayyukan yi wa makiya zagon kasa da kungiyoyin leken asiri,” in ji hukumar a cikin wata sanarwa.
An fitar da sanarwar ne a daidai lokacin da wani jami’in ma’aikatar harkokin cikin gida ta Ukraine ya bayar da rahoton faduwar lamarin a garin Shchastya da ke hannun gwamnati a baya, da ke a gabas da yankin ‘yan tawaye.
An bayar da rahoton cewa, jiragen saman Rasha sun kai hari a wani katafaren gida da ke kudancin Kharkiv na kasar Ukraine