A kokarinsa na samar da agaji ga rayuwar al’ummar mazabar sa dake shiyyar sanatan Sokoto ta Arewa a gundumar Mabera, Sanata Aliyu Wamakko ya baiwa al’ummar yankin Mabera na’urar rarraba wutar lantarki ta taransifoma mai karfin KVA 300.
Wadanda suka ci gajiyar wannan karimcin na zaune ne a kusa da masallacin Juma’a na Sheikh Musa Ayuba Lukuwa da ke karamar hukumar Sakkwato ta Kudu, kamar yadda Tribune Online ta rawaito.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: NASS ta Mika Sunayen Ministoci 45 da Aka Tabbatar Zuwa Fadar Shugaban Kasa
Alhaji Ahmed Baba Altine, wanda ya wakilci Sanata Wamakko a wajen gabatar da na’urar taranfoma ya bayyana cewa, wannan shiri na daga cikin hakin daya rataya a wuyan Sanata Wamakko.
Ya kuma jaddada cewa wannan karimcin ci gaba ne na kokarin Sanata Wamakko na ganin cewa al’ummar mazabar sa a kodayaushe suna cin moriyar dimokradiyya.
Baba Altine ya bayyana cewa tallafin ya biyo bayan korafin da al’ummar yankin suka kai wa Sanata Wamakko, a cikin karamcin da ya saba yi, ya bayar da umarnin a samar da na’urar taransfoma mai karfin KVA 300 domin rage musu kalubalen da ya shafi wutar lantarki.
Ya kara da cewa mazauna yankin sun dade suna fama da matsalar karancin wutar lantarki. Ya ƙarfafa su da su yi amfani da kayan aikin da aka ba su cikin gaskiya da kiyaye shi don ingantaccen amfani.
Da suke jawabi a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Sani Marshall da Zayyanu Yahaya sun bayyana jin dadinsu da yadda Sanata Wamakko ya nuna a kan lokaci. Sun koka da dadewar su cikin duhun da suka sha saboda rashin wutar lantarki.
Sun yabawa Sanata Wamakko bisa wannan alherin da ya nuna, sun kuma bayyana cewa wannan kokari na daya daga cikin da yawa da Sanatan APC yayi na samar da muhimman ababen more rayuwa da zasu inganta rayuwar al’ummar jihar, koda bayan ya rike Gwamna.
Sun yi alkawarin yin amfani da kayan aikin da aka samar domin ci gaban al’ummar Mabera Masallacin Lukuwa.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Karar Matawalle da EFCC, ICPC
A ranar Talata ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 30 ga watan Agusta, 2023, domin yanke hukunci kan karar da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya shigar, na neman dakatar da binciken da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ke yi a kan aikinsa da kuma sauran abubuwa.
A cikin karar tare da ambato: FHC/ABJ/CS/753/2023, Hukumar SSS, Rundunar ‘Yan sandan Najeriya, Hukumar ICPC Hukumar EFCC, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya sune a matsayin na farko zuwa na shida wadanda ake tuhuma.