Bayan kwashe kwanaki goma ana gwabza fada a Sudan, Amurka ta ce bangarorin da ke gaba da juna sun kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta na kwanaki uku da za a fara a ranar Talata,Daily Post ta rawaito.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, “Don tallafawa kawo karshen fadan, Amurka za ta hada kai da kawayenta na shiyya-shiyya da na kasa da kasa da kuma masu ruwa da tsaki na farar hula na Sudan don taimakawa wajen samar da wani kwamiti da zai kula da shawarwarin, da kammalawa.” da aiwatar da tsagaita bude wuta na dindindin da shirye-shiryen jin kai a Sudan”.
KARANTA WANNAN LABARIN: NPC Ta Musanta Yi Mata Kutse A Sabarta
Blinken ya kara da cewa, Amurka za ta yi aiki tare da bangarorin Sudan “zuwa burin da zai koma gwamnatin farar hula a Sudan.”
Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ta ce za ta kwashe sama da ‘yan kasarta 2,000 daga Sudan da ke fama da yaki a ranar Talata.
Daraktan ayyuka na musamman, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) Onimode Bandele, a wata hira da gidan Talabijin na Channels, ya tabbatar da cewa za a kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan ranar Talata.
Fadan da ake gwabzawa tsakanin bangarorin biyu, da sojojin Sudan da dakarun gaggawa ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane a Sudan.
Sojojin Sudan karkashin jagorancin Abdelfattah al-Burhan, da kuma RSF karkashin jagorancin Mohamed “Hemedti” Hamdan Dagalo, suna cikin yaki.
Yayin da yakin da ake gwabzawa tsakanin Janar-Janar din biyu,wasu kasashe da dama sun kwashe ‘yan kasarsu daga yankin.
Tun da farko dai, dakarun da ke gwabzawa sun kawo cikas ga shirin tsagaita bude wuta na Eid-el-fitr.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Tinubu da Mai Dakinsa Sun Diro Najeriya Daga Ƙasar Turai
Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya isa Abuja, babban birnin tarayya, a yau Litinin.
Jirgin Tinubu ya sauka ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, da ke Abuja, kuma ya samu tarba daga dimbin magoya bayansa.
Comments 1