A ranar Litinin din da ta gabata ne jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta tantance kashin farko na masu neman taka takara shugabancin kasar nan, a Babban zaben shekarar 2023 Mai zuwa.
Jimillar mutane 23 ne dai za su halarci tantancewar, wanda za a kammala a yau Talata.
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, John Oyegun, shi ne shugaban kwamitin tantancewar.
A halin da ake ciki, jam’iyyar ba ta bayyana matsayinta ba kan ko za ta kemance tikitin takarar shugaban kasar ne ga Wani shiya na daban dake kasar nan.
A cewar Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, za a dauki matakin ne bayan kammala aikin tantancewar.
Sai dai tun da fari an tsara fara Tantance masu Neman takarar da za’a fara Tantancewar a jiya Litinin ne kamar haka:
Chukwuemeka Nwajiuba
Badaru Abubakar
Robert A. Boroffice
Uju Ken-Ohanenye
Nicholas Felix
Dauda Umahi
Ken Nnamani
Tunde Bakare
Ibikunle Amosun
Bola Tinubu
Ahmad Rufai Sani
Rotimi Amaechi
Wadanda za a tantance ranar Talata su ne:
Dimeji Bankole
Kayode Fayemi
Godswill Akpabio
Yemi Osinbajo
Rochas Okorocha
Yahaya Bello
Sunan Jack-Rich
Christopher Onu
Ahmad Lawan
Ben Ayade
Ikeobasi Mokelu