By Ishaq Dabai
Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa FRSC tace tafiye tafiyen cikin dare yana da hadari ga masu tuka ababen hawa da masu tafiye tafiye, musamman yanzu da galibin hanyoyin ke cikin mawuyacin hali da rashin tsaro.
Kwamandan hukumar FRSC na jihar Kogi, Mista Solomon Agure,shine wanda yayi wannan ikirarin a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin a Lokoja.
Agure yace babu kyakkyawar gogewar hanya da zata iya fitowa daga yin saurin gudu wajen wuce gona da iri, amfani da waya yayin tuki, amfani da motocin dake da ƙarancin injina, rashin amfani da bell wanda yin hakan yake haifar da afkuwar hatsari.
Ya bukaci masu ababen hawa dasu guji cin karensu ba babbaka don kaucewa hadarurruka, a cewarsa, ya kamata direbobi su guji sabawa dokokin hanya da aka bayyana da sauran munanan abubuwan da suka shafi tsaro.
Sannan ya kara da cewa hukumar za ta zura ido don tabbatar da bin ka’idojin tsaron tuki da bin umarni a kan manyan hanyoyin.
Kazalika yace rundunar na shirin tura sama da ma’aikata 800, motocin sintiri 20, motocin daukar marasa lafiya hudu da manyan tireloli don kula da zirga zirgar ababen hawa.sannan “Yana da niyyar tabbatar da sanya shingayen binciken hanya, toshewar hanzari da amsa kiran damuwa don kowa ya sami ƙwarewar amfani da hanya da kuma bayan lokacin,” in ji shi.