“Taimakon ƙasashen yamma ba zai iya dakatar da juyin mulki a Afirka ba”
Wani babban Malamin Coci Bisi Olujobi na Cocin Wisdom Church of Christ International ya bayyana cewa tsoma bakin ƙasashen yamma ba zai iya ceto ƙasashen Afirka daga ƙarin juyin mulki ba.
Olujobi ya ce hanya daya tilo da za a dakatar da kwace madafun iko da sojoji ke yi ba bisa ka’ida ba, wato Coup, ita ce shugabannin Afirka su yi abin da ya dace wajen yi wa jama’a hidima tare da ba su damar morar romon Dimokuraɗiyya.
DAILY POST ta tuna cewa sojoji sun karbe ragamar mulki kwanan nan a Nijar da Gabon a daidai lokacin da ‘yan kasar suka nuna farin cikin su akai maimakonsa da su yi Allah wadai da juyin mulkin.
Da yake magana a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai Olujobi ya sake nanata vewa kamar yadda yake yawan faɗa a lokuta daban-daban a yayin zaman Coci, ya zama dole shugabanninmu su fara yin abin da ya dace ta hanyar yi wa jama’a hidima da zuciya daya.
KARANTA NAN:Rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara za ta ɗauki Jami’an rundunar haɗin guiwa ta farin kaya 4,300
Olujobi ya ci gaba da cewa kokarin da ƙasashen yammacin turai ke yi na dakatar da mulkin soji a Afirka ba zai yi nasara ba idan shugabannin Afirka suka ki aiwatar da dimokaradiyya ta gaskiya da za ta amfanar da talakawa.
Da yake magana kan zaben Gwamnan Kogi mai zuwa, Malamin Cocin ya bayyana cewa “ya hango canjin mulki a Jihar Kogi a zaɓen Gwamnan da za a yi a watan Nuwamba.
Ya ce dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Kogi Usman Ododo “ba shi da damar yin nasara a zaben sai dai wani abin al’ajabi na yanayin siyasa ya faru.
Ya yi hasashen cewa wata jam’iyya za ta karbe kujerar Gwamnati daga hannun APC a Jihar ta Kogi.
Sai dai ya buƙaci mutanen Jihar Kogi da su ƙara ƙaimi wajen gudanar da addu’o’i da kuma sanya kula wajen ƙare akwatunan zabensu a lokacin zaɓen domin gujewa maguɗi.
A wani labarin kuma, Olujobi ya bukaci Olugbo na Masarautar Ugbo ta Jihar Ondo, Oba Fredrick Obateru Akinrutan da ya yi addu’a gadan-gadan yana mai jaddada cewa “Na ga wani katsalandan da ake kullawa a masarautarsa.
Ya ce “Ya kamata mutum ya rika lura da bayansa yayin da makiya ke ta kokarin tada zaune tsaye a Masarautar sa Akinrutan ya kuma yi addu’a domin neman tsari akan ƙalubalen kiwon lafiya.