Kasar Burundi ta haramta amfani da Adai-daita sahu, da duk wasu nau’in abun hawa mai kafa biyu ko uku wajan Sufurin mutane a Babban Birnin kasar watau Bujumbura
Kekuna na kashin Kai, da kuma mashina dukkannin na daya daga cikin abubuwan da aka haramta amfani da su a babban birnin.
Kana an girke jami’an tsaron yan sandan kasar a hanyoyin shiga Bujumbura domin tabbatar da wannan doka.
Sai dai kafin yanke wannan hukuncin gwamnatin kasar ta Burundi ta bayyana cewa, Matuka irin wadannan ababen hawa da aka haramta ne ke haddasa akasarin haddauran da ake samu akan titunan birnin.
Rahotanni sun nuna cewa, akwai akalla mutane 600,000 da suka dogara da amfani da irin wadannan ababen hawa domin gudanar da harkokin su na yau da kullun a babban birnin Bujumbura. Yayin da Mafi yawaicin matukan matasa ne da suka fito da ga kauyuka domin samun aikin yi.