Daga Zubairu Lawan
A wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar na tattauna da wata mata da ta sheda cewa talauci ke dakushe karatun mata a Arewacin Najeriya.
Wata mata mai suna Farida Adamu wacce take zaune a jihar Kebbi, kuma mijin ta ya mutu ya bar mata yara, ta nuna cewa talauci ne ya dakushe karatun ‘ya’ya mata.
Ta bayyana cewa ‘yar ta ta fari ta yi aure ba tare da ta sami ilimin zamani ba. Ita kuma daya ‘yar ta ta yanzu haka Makarantar Islamiyya kawai take iya zuwa saboda rashin kudi.
Farida Bazaurace wanda take zaune a garin Kawara-manu mijinta ya mutu ya barta da yara biyar ita take kula da cinsu da shansu.
Farida tana da kananan yara guda uku wanda yanzu haka basu iya zuwa makarantar Boko sakamakon kasuwancin da take yi, bai taka kara ya karya ba.
Farida ta bayyana cewa koda zata iya sanya yaranta mata a makaranta dole tana bukatar #24,000 da zata saya masu kayan makaranta da kuma abinci da zasu rika ci a duk lokaci.
Binciken ya nuna cewa Nijeriya ce kasar da ilimin yara kananan yake koma baya. Ana kiyasta cewa akwai yara sama da miliyon 13.5 da basu zuwa makarantu sakamakon matsalolin rayuwa.
Yanki Birnin Kebbi da Sokoto da Zamfara da Katsina lamarin yana kara zurfafa rashin samun ilumin yara mata masamman a yana yin da yanzu kasar ke ciki.
Kimanin yaran da a yanzu suka rasa matsugunai a kauyukansu sun haura 501,574.
Hukumar kula da yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ta nuna damuwa da halin da yara kanana ke fuskanta na rashin samun karatu.