A wannan tattaunawar da wakilinmu ya bibiya a gidan rediyon Freedom da ke Kano, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matsayarsa kan batun cire tallafin man fetur, yanayin lafiyarsa da sauran batutuwan da suka shafi yakin neman zabensa.
Ranka ya dade na gane kana Saudi Arabia?
Eh ni a Saudiyya nake. Tafiya ce ta sirri. Tafiya ce don jaddada imanj. Ina son zuwa yin umra lokaci-lokaci. Wata dama ce ta dangantaka da Allah Ta’ala. Muna bukatar jagorancinsa. Najeriya na bukatar addu’a, shi ya sa muke nan muna yi wa kasarmu addu’a, kai da al’umma.
KU KARANTA KUMA Karya Ne Ban Gana Da gwamnonin PDP A Birtaniya Ba — Tinubu
Yaya yakin neman zabe ke tafiya zuwa yanzu?
Ya zuwa yanzu, yana yin kyau. Muna isa ga kowane dan Najeriya. Mun yanke shawarar cewa tarurruka ba su isa ba ko da yaushe. Muna bukatar mu hada dukkan ’yan Najeriya daga kowane bangare na kasar nan da kuma dukkanin bangarorin rayuwarmu ta zamantakewa da tattalin arziki. Mun hada ’yan kasuwa, manoma, masu hakar ma’adinai, masana’antu, masu nishadantarwa, shugabannin kwadago, da sauransu.
Ta hanyar alkawurran da muke yi a bayyane yake cewa za mu ci wannan zabe. Yayin da zabe ke gabatowa alamu sun bayyana a fili kuma shi ya sa abokan adawar mu ke ta tada hankali. A yanzu sun koma yin satar labaran karya da nakalto wasu maganganuna ba tare da tuntuba ba don kawai su ci zarafi.
Kamar me, Mai girma dan takara?
Kwanan nan an tambaye ni game da cire tallafin man fetur, na ce zan tabbatar da mun kawo karshen almubazzaranci da kuma sake tura kudaden ga mutanen da suke bukata da gaske. Wannan matsayi daya ne da kusan dukkan ’yan takarar suka hade kansu. Duk mun yarda cewa ana cin zarafin tsarin tallafi kuma yana fifita masu hannu da shuni fiye da talakawa. Dole ne a cire.
Ba zan iya adawa da mutanen da ke bayyana matsayinsu kan wannan ba. Na yi imani da tuntuɓar juna da lamuni ta dabi’u da ƙa’idodi na demokradiyya. Ina mutunta ra’ayin mutane kuma ba zan kasance cikin masu hana ra’ayi na rashin amincewa ko wata zanga-zangar da bata dace ba. Ni da kaina tsohon me zanga-zangar ne. Don haka me zai sa na ce kada mutane su shiga zanga-zanga da kyakkyawar niyya? Babu wani uzuri ga hakan kuma babu wani amfani da ikon da aka yi niyya.
Wasu mutane sun ce kuna tserewa daga yin hulɗa kai tsaye da ’yan Najeriya, musamman ta hanyar tattaunawa da manema labarai…
Me kuke nufi? Shin yanzu ba mu yin hira? Na gama magana da mutane ta taron zaure da magana kai tsaye da mutane. Waɗanda suke faɗin haka sun yi hasãra kuma sũ ne mãsu hasãra.
Har yanzu akwai raderadi game da lafiyar ka. Shin da gaske ka dace da shiga fadar shugaban kasa?
Ah! Na gaya muku inda nake yanzu. Na gama yin umrah. Na yi zagaye bakwai na dawafi, na yi tafiya bakwai tsakanin safa da Marwa. Shin marar lafiya zai iya yin haka? Wato tsautsayi ya dan uwa. Mutanen da suke yin wannan baƙar magana ba abin da za su ce sai ƙarya da shurme.
Na zagaya, na yi magana a dandamali daban-daban kuma na tsaya na sa’o’i don yin magana da masu sauraro daban-daban. Kafin su ce ba zan iya tafiya ba, sai su ce ba zan iya tsayawa ba, sun ji kunya. Tun lokacin da aka fara yaƙin neman zaɓe na haɓaka ra’ayoyi na asali fiye da kowa. Na nuna ilimi, gogewa da iyawa don kasancewa a kan al’amura a cikin ƙasa.
Kuma wannan aikin ya shafi ra’ayoyi da batutuwan da suka shafi shugabancin kasarmu. Ina da duk abin da ya kamata na zama shugaban Tarayyar Najeriya kuma ina rokon jama’ar kasar nan da su kasance masu kwarin gwiwa da mutunta hakan, ku dubi tarihina da ayyukan da na yi a baya. Ina so in yi wa kasa hidima kuma in yi wa kasa hidima sosai.
A Wani Labarin Kuma An Nada Tsohon Gwamnan CBN, Da Wasu 21 Mukaman Gargajiya A Kano
Al’ummar Tudun Wada da ke karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano, a kokarin da suke na karfafa saratu da dabi’un gargajiya, sun yi wa al’ummarsu 22 nadin rawani masu daraja daban-daban.
SOLACEBASE ta ruwaito daga cikin wadanda aka yiwa rawani da mukaman gargajiya sun hada da tsohon babban bankin Najeriya CBN, mataimakin gwamna, Alhaji Ahmad Garba a matsayin Wambai na Tudunwada, Janar Umar Usman mai ritaya a matsayin Walin Tudunwada, da Kanar Yakubu Bako a matsayin Danmajen Tudunwada.