Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya ce ya gaji baitul mali babu ko naira daga hannun magabacin sa, Aminu Tambuwal.
Aliyu ya ce Tambuwal ya kasa mika masa kwabo guda daga cikin gimbin arzikin da Allah yayiwa jahar ta Sokoto
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake karbar mataimakin kakakin majalisar wakilai Benjamin Kalu a ranar Alhamis.
Da yake amsa tambaya kan yadda ya gudanar da ayyuka 100 a cikin kwanaki 100 na farko a kan karagar mulki, Aliyu ya ce sai da ya hau kujerar mulki ya yi sadaukarwa da kuma jajircewa akan abinda ya iske gwamnatin jahar.
Karanta nanYadda Gwamanatin Jahar Kano Ta Aurar Da Zawarawa 1800 A Kashin Farko
Da yake magana ta bakin mataimakinsa, Idris Gobir, gwamnan ya ce mun gaji baitulmali da babu abin da za mu iya nunawa babu naira ko daya da aka mika mana mun yi sadaukarwa don sauya labarin jihar, kuma mun yi nasarar canza shi a cikin kwanaki 100 da suka gabata.
Ya bayyana dangantakar da ke tsakanin gwamnatin jihar da majalisar a matsayin mai kyau, inda ya ce shugaban jam’iyyar APC na jihar a yanzu, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ne ya shirya su.
A wani labarin kumaMatata Ta Shekamun Man Gyada Mai Zafi, Ta Suburbudeni da Guduma – Magidanci Ya Koka
Aliyu ya godewa shugabannin jam’iyyar Green Chamber da suka aike da tawaga mai karfi domin ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar bisa rasuwar abokin aikinsu kuma mamba mai wakiltar mazabar Isa-Sabon Birni na tarayya, Jelani Danbuga.
Ya bayyana marigayi dan majalisar a matsayin mai kishin kasa kuma cikakken mutumi wanda mutuwarsa ta zamo rashi ga kaftanin kasar Najeriya ba jahar Sokoto kawai ba.