By Abbas Yakubu Yaura
Adadin wadanda suka mutu a hare-haren ‘yan bindiga na baya-bayan nan a kananan hukumomin Illela da Goronyo a jihar Sokoto ya kai mutane 43.
Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari garuruwan da wasu kauyukan dake kusa da Ilella a safiyar ranar Litinin.tun da farko dai sun kashe mutane goma sha biyar, sannan kuma 12 a Ilella, mutane uku a karamar hukumar Goronyo.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a lokacin ziyarar Gwamnan a ranar Laraba, adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 43.Kauyukan dai da aka kai harin sun hada da, Kalmalo, Munwadata, Sarma, Runji, Tunbulunkun, Tafkin Taramniya, da Masasa, inda wani hakimin kauyen ya samu rauni a saka makon harin.
Gwamna Tambuwal da yake jawabi ga mutanen da suka rasa rayukansu a garin Ilella yace, “ a madadin gwamnati da al’ummar jiharmu ta gari, muna jajantawa kan wannan mummunan lamari daya ci rayukan ‘yan kasar da dama.“Wannan ba karamin lamari ba ne. Abin takaici ne, wannan lamari ya taba mu sosai.”
Sai dai ya yabawa hukumomin kananan hukumomi da sarakuna da shugabannin al’umma bisa yadda suka kafa kungiyar sa kai dake aiki tare da jami’an tsaro a yankin bisa halal.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma baiwa iyalai da ‘yan uwa hakurin rashin da suka yi da kuma samun lafiya da sauki ga wadanda suka samu raunuka a gida da kuma asibitoci.