Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya nada kwamitin mika mulki mai mutane 28, domin saukakawa tare da gudanar da mika mulki ga gwamna mai jiran gado,Punch ta rahoto.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Sokoto ranar Litinin mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Alhaji Mainasara Ahmad.
KARANTA WANNAN LABARIN: Marafa Ya Amince Da Shan Kaye, Ya Sha Alwashin Ba Zai Taba Zuwa Kotu Ba
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa mataimakin gwamnan jihar Alhaji Munir Dan’iya da kuma sakataren gwamnatin jihar ne za su jagoranci kwamitin.
Kwamitin zai kuma tattara bayanai na nasarorin daga ma’aikatu, sassan da hukumomi suka samu daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Hakanan zai samu tare da yin nazarin rahotanni daga MDAs kan duk ayyuka da shirye-shirye masu gudana dangane da matakin aiwatarwa / bayanan kasafin kuɗi da sauransu, ”in ji ta.
Gwamnatin jihar ta ce kwamitin zai shirya cikakkun takardun mika mulki ga gwamnati mai jiran gado don shiryawa nan da ranar 15 ga watan Mayu.
Gwamnatin Jihar ta kara da cewa mambobin kwamitin za su shirya taron rantsar da shi da ya dace tare da hadin gwiwar tawagar gwamnati mai zuwa da kuma yin duk wani kokari na ganin gwamnati mai zuwa ta samu duk wani tallafi da ake bukata domin fara aiki da wuri.
Mambobin kwamitin sun hada da Abubakar Muhammad, shugaban ma’aikatan gwamnati da kuma Ali Inname, kwamishinan kudi na jihar.
Sauran sun hada da Bello Abubakar, Kwamishinan Ilimi na matakin farko dana Sakandare, Lema Abubakar, Kwamishinan Lafiya, Farfesa Aminu Abubakar, Kwamishinan Noma da Farfesa Abdulkadir Junaidu, Kwamishinan Lafiyar Dabbobi.
Sauran sun hada da, Isah Bajini, kwamishiniyar raya karkara, Farfesa Aisha Madawaki, kwamishinan ilimi mai zurfi, Aminu Bala, kwamishinan filaye da gidaje da Dahiru Yusuf, kwamishinan albarkatun ruwa.
A cikin jerin sunayen akwai Abubakar Maikudi, kwamishinan tsaro na cikin gida, Abdullahi Maigwandu, kwamishinan kananan hukumomi, Bashir Gidado, kwamishinan matasa da wasanni da Kulu Sifawa, kwamishiniyar mata.
Karin a jerin sunayen sun hada da, Kabiru Aliyu, mai ba da shawara na musamman (SA) SDGs, Chika Umar, SA a Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko, Dokta Amamatu Yusuf, SA SOCHEMA da Ibrahim Magaji, SA kan harkokin siyasa.
Sauran sun hada da Abubakar Mohammed, babban Sakatare na (Min. of Agric), Muazu Madawaki, babban Sakataren (Min of Internal Security), Arzika Bodinga, Sakatare (Min of Budget), Mahmoud Kilgori (A&GSD) da Naziru Bala (Majalisar Zartaswa).
Kwamitin ya na da Dahiru Abbas, Babban Sakatare ( Kudi), Bande Rikina, Babban Sakatare (Hukumar Gwamnati), da Abdulkadir Ahmad (Daraktan Tsaro), a matsayin Sakatare, Mataimakin Sakatare.NAN
A wani labarin kuma, Twitter Ta Dakatar Da Shafin Wanda Ya Fara Maganar Tinubu Na Da Shaidar Zama Dan Kasa Biyu
An dakatar da shafin Tuwita na fitaccen dan jarida David Hundeyin saboda ya wallafa bayanan sirrin zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Asabar.
An kulle asusun shafin Hundeyin kwanaki bayan ya yi zargin cewa Tinubu yana da shedar zama dan kasa biyu a Najeriya da Guinea.