Tarayyar Turai za ta kashe Yuro miliyan 5.4 don horar da malamai a Arewa maso Yamma
Kungiyar Tarayyar Turai, EU, ta sanar da saka hannun jarin Yuro miliyan 5.4 domin bunkasa kwazon malamai a yankin Arewa maso Yamma.
Kwamishiniyar EU mai kula da kawancen kasa da kasa Jutta Urpilainen ta bayyana haka a wajen kaddamar da shirin bada tallafin kudi na Euro miliyan 40 kan ilimi da karfafa matasa a yankin Arewa maso yammacin Najeriya ta hanyar shirin Global Gateway.
KARANTA WANNAN LABARIN:Zamu Kyautata Jin Dadin Sojojin Nijeriya-Hafsan Sojoji
A cewar Ms Urpilainen, zuba jarin ya yi daidai da kudurin EU na dakile yawan yaran da ba su zuwa makaranta a yankin Arewa maso yammacin Najeriya ta hanyar inganta samar da ilimi mai inganci da karfafawa matasa a yankin.
“Wannan bangaren yana cike da wani shiri na daban na Euro miliyan 5.4 da muka sanya wa hannu a yau, wanda aka sadaukar da shi ga malamai don burin gina juriyarsu da karfinsu a cikin yanayi mai wahala
“Dole ne mu tuna cewa babu ilimi ba tare da malamai ba don haka ne ma ya zama dole mu saka hannun jari a horar da malamai.
“Manufa ta uku na shirin namu shi ne, hakika yana ba wa matasa kwarin gwiwa da dabarun da suke bukata, samar da ilimin sana’a a matsayin inganta yakin neman sauyi don kalubalantar halaye masu cutarwa da karfafawa ,” in ji ta.
Uwargida Urpilainen ta ce, Tarayyar Turai ta yi daidai da bayar da ilmin sana’o’in hannu da horar da matasan Najeriya domin samar musu da sana’o’in da ake bukata domin yin fice a kasuwar kwadago.
“Wannan babban shiri da aka kaddamar a yau an tsara shi ne tare da hukumomin Najeriya don tabbatar da mallakarsu da kuma samar da isasshiyar amsa ga bukatun gida.