Dan sandan mai mukamin ASP, Babatunde Adebayo, ya shiga hannu ne bayan wani hotonsa da aka dauka a fakaice ya karade gari inda ya mola tabar wiwi yana kuma busa hayakinta a wurin wani taro.
A ranar Lahadi ne dai aka baza hoton hafsan dan sandan a kafofin sada zumunta, yana shan tabar wiwi, a tare da hoton aka rubuta “Hafsan dan sandan Najeriya yana shan tabar wiwi a bakin aiki a yankin Ijora, Jihar Legas.”
Wata sanarwa da Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Legas ta fitar ta ce ASP Adebayo wanda ke aiki da ofishin ’yan sanda da ke Shogunle a jihar ya shiga hannu kuma zai fuskanci hukunci bisa dokar aikin dan sanda.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Ƴan Bindiga sun sake kai hari a wani Ofishin Ƴan sanda a Anambra, sun kashe Jami’ai 4
Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legs, Abiodun Alabi, ya ba da umarnin a fara gudanar da bincike a kan ASP Adebayo ba tare da bata lokaci ba domin ya girbi abin da ya shuka daidai da matsayinsa.
“CP Alabi ya kuma gargadi kanana da hafsoshin ’yan sanda su guji duk wani abu na rashin da’a ko saba dokokin aikinsu, domin duk wanda aka kama zai yaba wa aya zaki,” inji sanarwar.